Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Was cewa, gobara ta tashi a cikin wani Hotel da maniyyata ke zaune a birnin makka mai alfarma, na kasar saudiyya.
Shi ma kamfanin Dillancin Labarun aransa ya nakalto cewa; Gobarar ta tashi ne a cikin wani Hotel da maniyyata daga wata kasar Asiya su ke zaune a cikinsa, abinda ya sa aka killace mutane 1028 daga cikinsa.
Kawo ya zuwa yanzu babu wani rahoto da ya ke nuni da asarar rayuka sai dai wasu mutane biyu sun jikkata. Tashi gobarar a cikin birnin na makka, ya zo ne kwanaki kadan bayan da wata na’urar daga kaya, ta fado akan maniyyata da dama tare da kashe fiye da mutane dari daga cikinsu.
A kan hakan kuma rahotanni sun ce a adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon faduwar abin daular kaya ya kai 107 yayin da wasu kimanin 238 suka samu raunuka.
3364537