IQNA

22:50 - September 19, 2015
Lambar Labari: 3365119
Bangaren kasa da kasa, miliyoyin mahajjata daga koina suna ci gaba da isa Makka mai alfarma domin gudanar da aikin hajjin wannan shekara.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Albawwabah cewa, bayan shudewar makonni biyu da faduwar na’urar daukar kaya kan alhazai a makka da ya kashe mutane 107 tare da jikkatar 230 ana ci gaba da isa domin aikin hajjin bana.

Fiye musulmi miliyan biyu ne a halin yanzu suka isa birnin Makka mai alfarma domin gudanar da ayyukan hajjin bana daga yankunan na cikin gida da kuma kasashen ketare.Hukumar da ke kula da ayyukan haji a kasar saudiyya ta ce kusan maniyyata miliyan daya da rabi ne suka isa birnin Makka daga kasashen ketare zuwa jiya Juma’a, amma adadin yana ci gaba da karuwa, inda zai kai miliyan biyu da doreya.Hukumar ta bayyana cewa an rage adadin maniyyata na shekarar bana daga kasashen duniya ne saboda ayyukan gyare-gyare da ake gudanarwa a haramin Ka’aba mai tsarki, wanda ake sa ran kammala shi a cikin ‘yan watanni masu zuwa.Hajin wannan shekara dai ta zo da wasu matsaloli da ya sanya wasu ke ganin ya dace a dauki mataki na karbar wadannan ayyuka daga mahukuntan kasar, a mayar da shi ga hannun kasashen musulmi baki daya.A ranar laraba mai zuwa za a gudanar da tsawyuwar arfa haka nan kuma ranar alhamis za ta zama idin layya inda alhazai za su yanka dabbobi kamar yadda ake yi a cikin wannan aiki na ibada.3364896

Abubuwan Da Ya Shafa: Mekka
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: