IQNA

22:53 - September 19, 2015
Lambar Labari: 3365120
Bangaren kasa da kasa, wasu daga malaman cibiyar Azahar da wasu daga cikin malaman musulmi sun bukaci da a gudanar da sauyi kan batun yadda ake tafiyar da lamarin hajji.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Shafaqna cewa, Sheikh Salman Muhammad babban mai baiwa ma’aikatar kla da harkokion addini a Masar shawara ya yi kakkausar ska dangane da abin da ya faru a Makka tare da bayyana cewa hakan aiki ne na ganganci da bai kamata  ayi shiri a kansa ba.Ashraf Fahmi shi ma daya ne daga cikin malaman cibiyar Azaha ya bayyana cewa abin da ya faru kan maniyyata babban abin bakin ciki ne, kuma matukar za a bar lamarin haka to tabbas zai kara faruwa, domin kuwa masu kula da lamarin suna yi masa rikon sakainar kashi, alahali wannan babban lamari ne da ya shafi akidar dukkanin musumi.Ali Larijani shugaban majalisar dokokin kasar Iran ya bayyana abin da ya faru da cewa abin takaici ne, kamar yadda wasu da dama daga cikin malaman shi’a suka nuna bacin ransu kan sakaci da rayuwar musulmi a wannan wuri mai alfarma.A sakamakon faduwar na’urar daukar kaya masu nauyi a cikin haramin kaba’a mutane 107 ne suka rasa rayukansu wasu kuma 238 suka samu raunuka.3365040

Abubuwan Da Ya Shafa: Mekka
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: