IQNA

Yahudawan Sahyuniya Suna Son Su Mayar Da Rikin Palastinu Na Addini

23:49 - September 21, 2015
Lambar Labari: 3365993
Bangaren kasa da kasa, kungiyar yanto palastinu daga mamaya ta bayyana cewa haramtacciyar kasar Isra’ila tana son ta mayar da batun rikicinta da palastinawa ya zaman a addini.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ma’a cewa, Sa’ib Uraikat babban sakataren kungiyar yanto palastinu daga mamaya ta bayyana cewa haramtacciyar kasar Isra’ila tana son ta mayar da batun rikicinta da palastinawa ya zama na addini bisa ga take-takenta.

Uraikat ya ce abin da yahudawan sahyuniyan Isra’ila suka yi kai farmaki kan masallacin Quds babban abin ban takaici ne, y ace ya zama wajibi kan dukkanin al’ummomin musulmi da larabawa da su safke nauyin da ya rataya kansu kan wannan batu.

A cikin ‘yan kwanakin nan yahudawan sahniya sun kai farmaki kan masallata  awannan masallaci mai alfarma, inda suka yi amfani da barkokon tsohuwa a cikin masallacin, tare da cin zarafin masallata da kuma keta alfarmar wurin.

A makon da ya gabata (Yahuda Vinstin) babban alkali haramtacciyar kasar Isra’ila ya bayar da umarni yin amfani da harsashi mai rai kan palastinawa, kuma ya bayyana cewa jifar sojojin Isra’ila da dutsi daidai yake da yaki a kansu.

A bangare guda kuma Riyad Mansur jakadan Palastinu a majalisar dinkin duniya ya bayyana rashin kasa tabuka komai wajen takawa Isra’ila birki kan ta’addancinta da cewa abin Allawadai ne.

3365732

Abubuwan Da Ya Shafa: palastinu
captcha