IQNA

Kwamitin Kare Masallacin Aqsa Ya Bukaci Musulmi Da Su Safke Nauyin Da Ke Kansu

22:04 - September 22, 2015
Lambar Labari: 3366438
Bangaren kasa da kasa, kwamitin taimakon masallacin Aqsa na palastinawa da ke yankin zirin Gaza ya bukaci musulmi da su safke nauyin da kensu na kare masallacin quds.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Alaqsa cewa, Marwan Abu Ras shugaban kwamitin palastinawa na kre masallacin Aqsa ya bayyana cewa, wajibi ne kan msuulmi su kare wannan masallaci mai alfarma.

A cikin bayani na bai daya da kwamitin ya fitar, ya bayyana cewa malaman addinin muslunci na palastinu su ne ya kamata su zama a kan gaba wajen kara wayar da kan al’ummominsu kan matsayin wanann wuri mai tsarki.

Haka nan kuma wajibi ne akndukkanin musulmi na sauran kasashen duniya da su dauki mataki na bai daya domin nuna cikakken goyon bayansu ga wanann wuri ta hanyoyin da suka sawaka, tare da yin Allahwadai da abin da yahudawa ke yi.

Tun bayan da yahudawan sahyuniya suka fara kaddamar da farmakin bayan nan sun jikkata tare da kame daruruwan musulmia  cikin wannan masallaci mai alfarma, tare da keta alfarmar wannan wuri alkiblar musulmi ta farko.

Bayanin kwamitin ya ce matukar dai musulmi bas u ike tsaye wajen kare masallacin quds d sauran wurare masu tsarki ba, to kuwa za su gaba da ganin wulkanci da tozarci a cikin rayuwarsu, sakamakon yin biris da kare wannan wuri mai alfama.

3366314

Abubuwan Da Ya Shafa: palastinu
captcha