IQNA

Wani Dan ta’adda Ya tarwatsa Kansa A Tsakiyar Masalata Idi A San’a

12:18 - September 24, 2015
Lambar Labari: 3366972
Bangaren kasa da kasa, wani dan ta’adda da ya yi jigidar bam ya tarwatsa kansa a tsakiya masallata a yau a cikin daya daga cikin masallatan birnin San’a.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Al’alam cewa, a lokacin da masallat suke tafiya zuwa masallaci a birninsan’a fadar mulkin kasar wani dan ta’adda ya tayar da bam a cikin masallacin safiyah da ke birnin.

Bisa ga wannan rahoto akalla mutane 10 nes uka yi shahda sakamakon hakan, yayin da wasu da dama kuma suka samu raunuka.

A daidai lokacin da abin ya faru jami’an tsaro sun samu wata mota da aka shakare da bm a kusa da masallacin na safiyya da ek shirin tarwatsa ta amma an asam damar lalata kayar da suke fashewa a cikinta.

An bayyana cewa daga bisani za a bayar da cikakken bayani dangane da hakikanin abin da ya faru.

3366952

Abubuwan Da Ya Shafa: yemen
captcha