IQNA

An Sanar Da Adadin Dukkanin Mahajjatan Shekarar Bana

12:21 - September 24, 2015
Lambar Labari: 3366973
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan kasar Saudiyya sun sanar da adadin dukkanin alahazai da suke gudanar aikin hajjin bana na 1436.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Al-alam cewa, adaddin dukkanin alahazan bana bai kai mutane miliyon 2 ba baki daya.

Kamfanin dillancin labaran kasar saudiyyah ya habarta cewa, adadin dukkanin alhazan bana daga ciki da wajen kasar ya kai miliyan daya da kubu dubu 952 da kuma 817.

Bayanin ya kara da cewa daga wajen kasar da suka zo daga kasashen duniya adadin ya kai miliyan daya da 384 da kuma 941, sai kuma 567 da kuma 876 daga cikin kasar da suka iso daga yanknan zuwa birnin Makka mai alfarma.

3366956

Abubuwan Da Ya Shafa: Mekka
captcha