IQNA

Nisantar Da Hankulan Musulmi Daga Palestine Shi Ne Babbar Manufar Kirkiro Kungiyoyi Irin Su Daesh

21:19 - September 28, 2015
Lambar Labari: 3373962
Bangaren kasa da kasa, Sheikh Muhammad Hussain babban mamali mai bayar da fatawa a birnin Quds ya bayyana cewa babbar manufar kirkiro kungiyoyi irin su Daesh shi ne nisantar da hankulan musulmi daga Palastinu da kuma barnar sahyniyawa.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na rtv.gov.sy cewa sheikh Muhammad Hussain  bababn malamin birnin na quds ya bayyana hakan ne sakamakon abububuwan da ske faruwa a halin yanzu a duniyar musulmi na tashin hankali da ta’addanci, sakamakon kirkiro kungiyoyin ‘yan ta’adda da aka yi da suke aikata ta’addanci da sunan musulunci.

Wanda a cewar malamin hakan ya manatar da al’ummomin larabawa abin da yake faruwa kan ala’ummar Paloastinu baki daya inda suka mayar da hankalinsu kaco kaf kan batun kungiyoyin da ke aikata ta’addanci da sunan wannan addini, wadanda wasu daga cikin gwamnatocin wadannan kasashe ne ma suke da hannu wajen kirkiro su da kuma daukar nauyins.

Ya ce hakikanin gaskiya abin da wadancan yan ta’addan suke aikatawa bas hi banvanci da abin da yahudawan sahyuniya suke aikatawa, dukkaninsu yan ta’adda ne mashaya jinin bil adama makasa mabarnata masu sabo a bayan kasa, bil hasali ma abin da yan ta’addan suke yi aiki ne da tsari na yahudawan sahyuniya suke aiwatarw3a.

Mai fatawar na Quds ya ce abin takaicin shi ne, su yan ta’addan Daesh sun dauka cewa addini ne suke yi, suna yin barana da kisan kai da zubar da jinin bayin Allah da su jib a su ganai ba, amma suna ganin daidai suke sakamakon muggan fatawoyi da aka ba su kan hakan, alhali suna cikin dimuwa ne sakamakon jahilci da rashin sanin addinin muslunci da kuma koyarwarsa.

3372224

Abubuwan Da Ya Shafa: palastinu
captcha