IQNA

Dole Ne A Mayar Da AyyuKan hajji Karkashin Kulawar Kasashen Musulmi

23:48 - September 29, 2015
Lambar Labari: 3374488
Bangaren kasa da kasa, cibiyar mabiya tafarkin iyalan gidan manzo a kasar Moroco ta bayyana cewa ya zama wajibi a karbe batun gudanar da ayyukan hajji daga masarautar Al Saud.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na mamlakapress.com cewa, ya zama wajibi a dauki matakai na gaggawa domin kwace dukkanin ayyukan da suka shafi haji daga hannun masarautar Al Saud sakamon abin da ya faru na kisan jama’a a Mina a wannan shekara kamar yadda duniya ta sheda.

Anasa bangaren shima shugaban jamhuriyar muslunci ya fadi yanzu a gaban babban taron majalisar dinkin duniya cewa; dole ne masarautar iyalan gidan Saud ta bari a yi bincike kan hakikanin abin da ya faru a Mina, kuma binciken ya hada da bangarori daban-daban na kasashen musulmi, sakamakon da binciken ya bayar shi ne duniya za ta gamsu da shi.

Shugaban hukumar alhazai ta kasar Moroco ya bayyana cewa, akwai sakaci matuka daga mahukuntan Saudiyya kan wannan lamari, saboda haka yana da kyau a dauki dukaknin matakan da suka dace domin shawo kan wannan lamari.

Muhammad Bu Said ministan kudi da tattalin arziki na kasar ta Moroco, shi ma ya bayyana takaicinsa matuka dangane da abin da ya faru, musamman ma ganin yadda mahukuntan kasar ta Saudiyya ska yi ta yi wa al’ummomin duniya yawo da hankali kan batun abin da ya faru a Mina, inda aka kashe mutane amma ba tare da wani Karin bayani ba.

Shugaban tawagar mahajjatan kasar Morocco kuma ministan tattalin arzikin kasar Muhammad Bu-Sa’eed ya koka kan yadda jami’an gwamnatin kasar Saudia suke mu’amala da jami’an kiwon lafiya na sauran kasashen musulmi  kan bin ya faru a Mina.



Yana cewa jami’an gwamnatin kasar Saudia sun ki amincewa jami’an kiwon lafiya na kasar Morocco su isa wararen ajiye gawawwaki don gano mutanen kasar da aka rasasu bayan hatsarin na Mina.



3374038

Abubuwan Da Ya Shafa: Mekka
captcha