Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo nan a bangaren hula da jama’a na cibiyar musulmin kasar Birtaniya cewa, wannan cibiya tana isar da sakon ta’aziyya ga dukkanin iyalan wadanda suka rasa rayukansu daga cikin alhazan bana.
Bayanin ya ce za a zaman makoki kan wannan lamari domin adu’a ga wadanda suka yi shahada a shekarar bana a lokacin hajji, inda dubban alhazai suka rasa rayukansu sakamakon abin da ya faru a Mina.
Sakon cibiyar ya hada da addu’a kan Allah madaukakin sarki ya gafarta ma dukkanin muuslmin da suka rasua wannan balai mai girma da ya faru kan al’ummar musulmi.
A taron da za a gudanar, za a gabatr da jawabai a wurin, inda Hojjatol islam Muhammad Ali Shemali zai gabatr da jawabi na karshe a wurin.
3375756