IQNA

Hudubar Ghadir Alkawali Ne Na Dukkanin Musulmi

23:26 - October 02, 2015
Lambar Labari: 3377427
Bangaren Ilimi, lamarin tarikhi ya tababtar da wannan ranar babban idin al'ummar annabi ranar da Manzon Allah (s) ya nada Aliyu bn Abi Talib a matsayin magajinsa kuma shugaban musulmi a bayansa.


Faidollah Akbari daya daga cikin mambobi na tawagar jami’ar muslunci a zantawarsa da Ikna ya bayyana cewa, a hakikanin gaskiya ranar Ghadir ta ayyana Imam Ali (AS) tana a matsayin wata rana mai muhimmancin gaske ga tafarki da kuma ci gaban Musulunci saboda matsayin da take da shi na ranar da aka mika ci gaban jagorancin Musulunci a dukkan bangarori da kuma jagorancin al'ummar musulmi ga hannun wani mutum Iamm Ali (AS), wanda ba shi ne ya zo da sakon ba, duk kuwa da irin yanayi da barazanar da suke fuskantar al'umma daga ciki da waje, da kuma cewa a wancan rana ce Allah Ya cika ni'imarsa ga al'umma da kuma zaba musu Musulunci a matsayin addinin da ya yarda su bi.

Hakan kuwa saboda a daidai wannan lokaci jagorancin Musulunci da musulmi bayan Ma'aiki yana bukatuwa da wani mutum da ke da irin siffofin da Manzo yake da su, saboda wasu dalilai, ciki kuwa har da cewa kusan dukkan lokacin da Manzo ya shafe a Makka da Madina lokaci ne da ke cike da matsaloli irin su tsangwama, yake-yake da sauran matsaloli na cikin gida.

Don haka Musulunci yana bukatar wani mutum tsayayye wanda zai ci gaba da shiryar da al'umma kamar yadda Manzo ya yi.Don haka muna taya dukkanin al'ummar musulmi musamman mabiya tafarkin Ahlulbaiti murnar wannan rana mai albarka wacce Manzo ya bayyana ta a matsayin babbar ranar idin musulmi.

A matsayinmu na musulmi, mun yi imani cewa addinin Musulunci addini ne da aka sauko da shi ga dukkan bil'Adama sannan kuma shari'arsa ta kumshi dukkan abin da dan'Adam yake bukata a rayuwarsa ta yau da kullum. Kamar yadda kuma muka yi imani da cewa gudanar da wannan shari'a da jagorancin al'umma yana hannun wanda yazo da sakon ne wato Manzon Allah (s.a.w.a) matukar dai yana raye, wannan lamari ne da dukkan musulmi suka hadu a kansa. Abin tambaya da kuma kace nacen shi ne yadda lamarin zai kasance a bayansa.

Mabiya Ahlulbaiti (AS) sun yi amanna da cewa ayyana wanda zai gaji Ma'aiki (s.a.w.a) wajen gudanar da wannan aiki nasa ba yana hannun kowa ba ne face Allah da ManzonSa (s.a.w.a), wato a takaice dai al'umma ba su da bakin magana cikin wannan lamari kamar yadda ba su da bakin magana wajen zaban wanda zai zo da sakon Allah Madaukakin Sarki wato Annabi "Allah Shi ne Mafi sanin inda Zai ajiye Manzancinsa.

Don haka imamanci ko kuma halifanci a matsayinsa na ci gaban aikin annabtaka, shi ma Allah da ManzonSa ne suka san inda za su ajiye shi. Ahlulbaiti (AS) da mabiyansu sun yi amanna da cewa halifanci ko kuma jagorancin al'umman musulmi bayan Ma'aiki wani matsayi ne mai girman gaske don haka babu yadda za a yi Allah da ManzonSa su bar shi a hannun mutane haka kawai musamman idan aka yi la'akari da yanayin siyasa da zamantakewa da Musulunci yake fuskanta a lokacin, don haka suka ce Allah da ManzonSa ne kawai za su zabi wanda zai rike wannan matsayi.

Dangane da tambayar farko mabiya Ahlulbaiti (a.s) sun yi imani da cewa tun ranar gini ranar zane, tun farko-farkon wannan sako na Musulunci Allah da ManzonSa suka zabi mafi daukakan wannan al'umma bayan Manzo (s.a.w.a) a matsayin wanda zai gaje shi da kuma ci gaba da jagorancin al'umma bayansa, kuma sun ci gaba da bayyana hakan a lokuta daban-daban har lokacin karshe na rayuwar Ma'aiki. Wanda kuwa aka zaban shi ne Amirul Muminina Aliyu bn Abi Talib (AS). Batun yaushe da kuma ina aka yi zaben kuwa, to kamar yadda muka ce ne an fara wannan zabe ne tun ranar da aka umarci Manzon Allah (s.a.w.a) da ya kirayi makusantansa zuwa ga Musulunci ranar da ake kiranta da Yaum al-Inzar, wato lokacin da Allah Madaukaki ya saukar da ayar:

To wannan batu dai shi ne za mu yi magana a kansa da kuma ganin yadda ya kasance kamar yadda muka yi tambaya a kai a baya. Hakikanin manufarmu ba ita ce bayyana wa mai saurare kissar Ghadir da abubuwan da suka faru dalla-dalla ba ne, don kuwa mun sha yin hakan a shirye-shiryen da suka gabata, face dai babbar manufar ita ce fitar da wasu abubuwa muhimmai cikin wannan lamari da kuma bayyanar da wanda ya cancanci jama'a su koma gare shi bayan Ma'aiki (s.a.w.a), to amma don matashiya bari mu dan kawo abin da ya farun a gurguje.

Malaman tarihi da na tafsiri da ma na hadisi, yayin da suke magana kan wannan lamari da kuma abubuwan da suka faru sun bayyana cewa: A shekarar karshe ta rayuwarsa, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kuduri aniyar zuwa aikin hajji, abin da daga karshe ake ce masa Hajjin Ban Kwana.

Nan da nan labari ya yadu a duk fadin duniyar musulmi, al'amarin da ya sa da yawa daga cikinsu suka yiyo azamar kasancewa tare da Ma'aiki (s.a.w.a) cikin wannan aikin hajjin. An bayyana cewa adadin musulman da suka yi wannan aiki na hajjin ya kai dubu dari da ashirin. Bayan gudanar da aikin hajjin, sai Ma'aiki (s.a.w.a.) da mabiyansa suka kamo hanyarsu ta dawowa, inda suka iso wani guri da ake ce ma Ghadir Khum a ranar 18 ga watan Zil Hajjin shekara ta goma bayan hijira.

Shi wannan guri ya kasance wata mahada ce ta hanyoyin zuwa Madina, Iraki, Masar da kuma Yaman. A nan ne Ma'aiki (s.a.w.a.) ya yi ban kwana da sauran musulmi ya kama hanyarsa ta komowa gida (Madina) kana kuma sauran al'umma ma kowa ya kama hanyarsa. Jim kadan bayan ban kwana da kuma kama hanyar Ma'aiki (s.a.w.a.) zuwa Madina, sai ga Mala'ika Jibril (a.s.) da sako daga Allah zuwa ga ManzonSa, sakon kuwa shi ne ayar nan, wacce daga baya malamai suke kiranta da Ayatul Tabligh wato: " Ya kai Manzo ka isar da abin da aka saukar maka na daga Ubangijinka, idan baka aikata ba to ba ka isar da sakonSa ba, Allah Zai kare daga mutane. Lalle Allah ba Ya shiryar da mutanen da suke kafirai.

. Nan take sai Ma'aiki (s.a.w.a.) ya yi umurnin da a tsaya sannnan wadanda suka wuce su komo wadanda kuma ba su riga da sun iso ba a jira su su iso. Lokacin da kowa da kowa ya iso, sai Ma'aiki (s.a.w.a.) ya hau kan abin da aka tanadar masa don kowa da kowa ya gan shi, inda ya gabatar da dogon jawabi.

Daga nan sai ya daga muryarsa ya ce: "Hakika Allah ne Shugabana, ni kuma shugaban dukkan muminai, kuma ni ne nafi soyuwa gare su a kan kawukansu. To duk wanda na kasance shugabansa, to Aliyu shugabansa ne ... (ya maimaita hakan har sau uku). Ya Allah Ka jibinci wanda ya jibince shi kuma Ka ki wanda ya ki shi, Ka taimaki wanda ya taimake shi ka wulakanta wanda ya nesance shi, Ka sanya gaskiya tare da shi a duk inda ya juya.

Lalle wanda ya ke nan ya sanar da wanda ba ya nan". Jim kadan da gama wannan jawabi na Manzo (s.a.w.a), sai ga Mala'ika Jibril (a.s.) ya sauko da wata ayar, wacce daga baya ake kira da Ayar Cikan Addini wato fadin Allah (S.W.T) cewa: (A yau na cika muku addininku, kuma na cika muku ni'imata sannan kuma na zaba muku (addinin) Musulunci a matasayin addini) Daga nan sai Manzo (s.a.w.a) ya sauko jama'a suka zo suna taya Ali (a.s) murna da wannan matsayi da ya samu cikinsu kuwa har da halifa Abubakar da Ummaru.

A takaice dai wannan ita ce kissar Ghadir wacce ta kasance matsayar karshe da Manzon Allah (s.a.w.a) ya dauka don shiryar da al'ummarsa da kuma kare su daga rarrabuwa kan wanda zai gaje shi kamar yadda malaman hadisi da tafsiri suka tabbatar.

Dubi cikin wannan zabi da Manzo (s.a.w.a) ya yi wa Ali za mu ga tamkar yana so ne ya jaddada wa musulmi cewa Musulunci (musamman a daidai wancan lokaci) yana bukatar wani mutum mai ilmi sama da kowa, don kuwa jagoranci na bukatuwa da masaniya ta yadda za a iya bullo wa duk wani makirci da matsala gwagwardon yadda take bukata, wanda babu wanda yake da wannan siffa in ba Ali (AS) ba.

Ya jaddada cewa Ali na tare da gaskiya ta yadda babu yadda karya ko bata za ta iya kusatarsa, duk abin da ya yi riko da shi gaskiya ne duk abin da ya yaka kuwa karya da bata ce kamar yadda Manzo ya ce: "Ali na tare da gaskiya gaskiya kuma na tare da Ali (AS)".

Yana so ya fahimtar da mutane cewa babu wani mutumin da yake gani ya cancanci wannan matsayi na jagoranci da ci gaba da isar da sako sai Ali (AS). Yana so ne ya nuna wa mutane cewa Ali (AS) ya mallaki duk wata siffa daga cikin siffofin da yake da su na jagoranci don haka jama'a su bi shi sau da kafa kamar yadda suke binsa.Halifancin Manzon Allah (s.a.w.a) dai ya bambanta da sauran halifanci ko kuma shugabanci, don kuwa lamarin ba wai shugabanci ba ne kawai, face dai shiryarwa ce da kuma cimma manufofin Musulunci.

Ko shakka babu a wancan lokaci Musulunci na bukatar wani mutum kamar Manzo da zai ci gaba da wannan aiki, babu wani kuma a lokacin da ya cika wadannan sharudda in ba Aliyu bn Abi Talib (a.s) ba.

A takaice dai wannan shi ne abin da ya faru a yakin Khandak da ke nuna mana kadan daga cikin jaruntakar Ali (a.s). Akwai abubuwa da yawa da Imam Ali (a.s) yake da su da suka sanya ya cancanci halifanci da jagorantar al'umma sama da kowa daga cikin sahabbai, lokaci ba zai bari mu kawo su a nan ba sai ana iya komawa ga rayuwarsa don ganinsu.

3377224

Abubuwan Da Ya Shafa: ghadir
captcha