Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Saba net cewa, Abdulmalik Al-huthi a jawabinsa ga al’ummar Yamen bayan tsawon kwanaki fiye da dari biyu suna fuskantar hare-haren wuce gona da iri daga jiragen saman yakin gidan Sarautar Saudiyya da kawayenta.
Sayyid Abdul-Malik Huthi a jiya Talata ya fayyace irin kyakkyawar alaka ta kud da kud da ke tsakanin mahukutan Saudiyya da Yahudawan Sahayoniyya gami da irin taimakon makamai da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke gabatarwa ga Saudiyya domin murkushe al’ummar Yamen musamman rahoton baya-bayan nan kan irin tarin makamai masu linzami da gwamnatin h.k.Isra’ila ta jibge wa mahukuntan Saudiyya a sansanin Khamis Mushid da ke yankin Asir na kasar Saudiya.
Har ila yau Sayyid Huthi ya fayyace cewar babu mai kokwanto kan cewa ‘yan mulkin mallakar Birtaniya ne suka samar da gidan sarautar Ali- Sa’ud tare da share fage ga yahudawan sahayoniyya kan mamaye Palasdinu, inda a halin yanzu al’ummar palasdinu ke dandana kudarsu a hannun yahudawan sahawoniyya, kamar yadda al’ummar musulmi ke fuskantar dangogin masifun ta’addanci daga masarautar Saudiyya musamman ta hanyar yada akidar ta’addanci da karfafa ‘yan ta’adda a duniya.
Makiya mutanen yemen ne a karshe zasu yi asara a yakin da kasar saudia da kawayenta suka dorawa mutanen kasar, Abdul-Malik Al-Huthi shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ne ya bayyana haka a jiya Lahadi a wani jawabin da ya yiwa mutanen kasar ta tashar television na kungiyar.
Al-hutha ya kara da cewa mutanen kasar Yemen ne zasu sami nasara daga karshen don sun shiga wannan yakin ne don nemawwa kansu da kasarsu encin kai. Zasu sami nasara ne don su aka zalunta.
Danagne da abinda yake faruwa a birnin Aden wanda wasu sassansa da csuke karkashen ikon saudia da magoya bayanta kuma, Abdulmalik Al-Huthi ya ce, nasarar da saudia da samua a wani bangare da birnin Aden na wucin gadi ne da sannan zasu rasa wannan nasarar.
Mutane akalla dubu shida da dari biyar ne suka rasa rayukansu ya zuwa yanzu mafi yawansu mata da yara a hare haren na kasar saudia take kaiwa kan Yemen tun ranar ashirin da biyar ga watan Maris Maris da ya gabata.