IQNA

Ala’uddin Borujardi Ya Gana Da Sayyid ahssan Nasrullah Kan Halin Da Ake Ciki A Yankin

23:21 - October 16, 2015
Lambar Labari: 3386079
Bangaren kasa da kasa, shugaban kwamitin kula da harkokin siysar waje da kuma tsaron kasa a majalisar dokokin Iran Alauddin Borujardi ya gana da babban sakaraen kungiyar Hizbullah.


Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto dags hafin sadarwa na yanar gizo na tashar Almanar cewa, a yammacin jiya Alauddin Borujardi tare da Muhammad Fath Ali jakadan kasar Iran a Lebanon sun gana da Sayyid Hassan nasrullah.

A yayin ganawar tasu an tabo muhimman batutwa da suke da alaka da halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya da kuma kasar ta ta Lebanon.

Bayan kammala wata ziyara a kasar Syria da Alauddin Borjardi ya kai, daga can ya wuce zuwa birnin Beirut na kasar Lebanon.

Inda ya fara da ziyartar kabrukan shahidan gwagwarmaya, da hakan ya hada da kabarin Imam Mogniyyah, kafin daga bisani kuma ya gana da babban sakataren kungiyar Hizbullah, dangabne da lamurra da suke da alaka da halin da ake ciki a yankin baki daya.

3386054

Abubuwan Da Ya Shafa: lebanon
captcha