Kamfanin dillancin labaran Iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-kafil cewa, bangaren cibiyar da ke kula hubbaren Abbas (AS) da ke daukar nauyin buga tafsiran kur’ani mai tsarki za ta dauki nauyin shirya wata gasa ta bincike kan ilmomin kur’ani mai tsarki mafi girma bisa bahasin hadin saqalain.
Bayanin ya ci gaba da bababr manufar shirya wannan gasa dai it ace kara kara karfafa gwiwar masu bincike wajen fadada bicikensu kan lamurra da suka shafi mahangar kur’ani mai tsarki wajen tabbatar da hadisin manzo Allah kan iyalan gidansa (AS) wanda ke gwamanya su a matsayin nauyaya biy, kur’ani da kuma Ahlul bait (AS)
Haka nan kuma za abayar da dama zuwa wani kayayyaden lokaci da za a gudanar da bicike da kuma mika shi ga wannan cibiya, domin tantance dukkanin wadanda suka shiga gasar kuma suka kawo dukkanin abubuwan da ake bukata gwargwado domin tabbatar da hadisin.
Bisa ga bayanin cibiya ana bukatar abin da za arubuta kada ya gaza shafuka 150 tare da bayyana dalilai da kuma ambaton inda aka samo dalilai domin tabbatar da abin da mtum ya bicika kuma ya rubuta ya yi daidai da abin da ya nakalto.
Mutum na farko zai samu kyautar Dinari miliyan 8 na Iraki, na biyu kuma zai samu miliyan 5, yayin da na uku kuma zai samu miliyan 3 na dinari.
3384966