IQNA

An Fara Gudanar Da Wani Taro Na Tadabbur A Cikin Kur’ani A Morocco

22:12 - October 28, 2015
Lambar Labari: 3407229
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani zaman taro mai taken tadabbura a cikin kur’ani mai tsarki tare da halartar mutane fiye da 400 a birnin kzablanka na kasar Morocco.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alyaoum24 cewa, shi dai wanann taro ana gudanar da shi ne tare da kulawar babbar cibiyar kula da harkokin muslunci ta kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa kimanin mutane 400 ne da suka hada da manyan malamai da masana daga sassa na kasar da kuma wasu kasashen ketare, wadanda suke ci gaba da halaratr taron tare da gabatar da laccoci da kuma makalaoli na kara wa juna sani.

Da dama daga cikin kafofin yada labarai suna daukar abubuwan da suke wakana a wajen wanann taro suna yadawa v aciki da wajen kasar, duk kuwa da cewa akasarin madaba’ntu su ma ba a bar su a bay aba wajen daukar abubuwan ad suka gudana a wurin taron.

Ana ci gaba da gudanar da taron tare da sanya idon babbar cibiyar da ake kula da traukan tadabbr a cikin kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa, kuma ana sa ra kammala taron a cikin kwanaki biyu masu zuwa.

Daga cikin abubuwan da aka mayr da hankalia  akansu akwai bayani kan hakikanin abin da ake kira tunania  cikin ayoyin kur’ani mai tsarki, wanda shi ne zai bayar da dama zuwa ga hakinain tadabbur da ake Magana.

Domin kuwa wasu daga cikin wadanda suka gabatar da jawabi ko makaloli a wurin sun yi ishara da cewa, tunani shi kadai kan ayoyin kur’ani bas hi tadabbur ba, domin kuwa tadabbur yana zuwa a lokacin da ake tnani domin gano ma’anoni da hikimomin bangiji da suke cikin ayoyin da ake karantawa.

An dai gina wannan babbar cibiya ne tun a cikin shekara ta 1433 kuma ba ta gushe ba tana ci gaba da gudanar da ayykanta da kuma taruka na watanni da kuam na shekara a cikin kasashen musulmi.

3404945

Abubuwan Da Ya Shafa: morocco
captcha