IQNA

18:40 - October 30, 2015
Lambar Labari: 3417488
Bangaren kasa da kasa, an gane gawar Sayyid Haidar Alhani daya daga cikin manyan malaman shi’a a kasar Lebanon da ya rasa ransa sakamakon abin da ya faru a Mina.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «onlylebanon.net» cewa, bayan kwashe tsawon fiye da wata guda da faruwar kisan alhazai a Mina, an gane gawar Allah Sayyid Haidar Alhasani limamin masallacin kauyen Markaba a cikin gundumar Marja’iyyun a kudancin kasar Lebanon.

An gane gawar malamin ne bayan gudanar da bincike da gwaji na DNI, wanda iyalansa da danginsa suka tabbatar da cewa shi ne, kuma ana shirin dauko gawarsa zuwa mahaifarsa domin yi masa janaza.

3415425

Abubuwan Da Ya Shafa: Lebanon
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: