Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Tina cewa, a wanann maoo an gudanar da sallar Juma’a ayankuna daban-daban ne a kasar Lebanon.
Shugaban kwamitin tsaro da harkokin kasashen waje na majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran ya ja kunnen gwamnatin Saudiyya cewa zartar da hukuncin kisa a kan daya daga cikin manyan malaman Shi’a na kasar Sheikh Nimr Baqir al-Nimr za ta haifar da sabon rikici a yankunan da ‘yan Shi’a suka fi yawa a kasar.
Ayatollah Qabalan mataimakin shigaban majalisar shi’a a Lebanon shi ma a nasa bangare ya bayyana cewa, zartar da hukuncin kisar da aka yanke wa Sheik al-Nimr zai haifar da gagarumin rikici a yankunan ‘yan Shi’an wanda ko shakka babu hakan ba zai yi kyau ga gwamnatin ta Saudiyya ba, don kuwa babu abin da Shehin malamin yayi face wa’azi da magana.
Shi Ma Hojjatol Islam Sayyid Ali Fadlollah ya bayyana cewa, ko shakka babu abin da mahukuntan kasar Saudiyya suke na yin wasa da sunan bangaranci na addini domin cimam manufofi na siyasa lamari mai matukar muni, daga ciki kuwa har wannan hukuncin na siyasa da suka yanke kan Sheikh Nimr, wanda kuma zartar da shi zai jefa su cikin balai.
Da ma dai wannan dai ba shi ne karon farko da jami’an Iran daban-daban suka ja kunnen Saudiyyan kan aiwatar da wannan hukuncin ba, don bayan da aka tabbatar da shi a jiya akmar yadda majiyoyin suka tababtar.
Kuma adai a jiya ne dai dan’uwan Shehin malamin ya bayyana cewar kotun koli ta kasar Saudiyyan ta tabbatar da hukuncin kisan da aka zartar a kan Sheik al-Nimr din a watannin baya saboda abin da suka kira tada hankali da kuma tunzura mutane su yi bore wa sarkin kasar musamamn a yankunan gabaci.