IQNA

Taro Karo Na Hudu Kan Gajiyarwa Irin ta Kur’ani Da Sunna

22:31 - November 06, 2015
Lambar Labari: 3443995
Bangren kasa da kasa, an gudanar da zaman taro kan gajiyarwa irin ta kur’ani mai tsarki a jami’ar Bani Yusuf da ke kasar masar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Misral Yaum cewa, an gudanar da zaman taron ne tare da halartar wakilin Mustafa Al-shimi shugaban kungiyar Ijazul Kur’an ta duniya da ke Alkahira wanda Dr Abdul Muslih ya wakilta.



Amin Lotfi shugaban jami’ar Bani Yusuf ya gabatar da jawabi a wurin taron, inda ya bayyana cewa bababr manufar gudaar da irin wannan taro mai matukar muhimmanci shi ne, kara karfafa gwaiwar masu bincike kan lamurra da suka shafi kur’ani mai tsarki.



Ya ce ta irin wannan hanya masu bincike za su kara samun karfin gwiwa domin gudanar da bicike na ilimi a bangaren kur’ani da a sauran ilmmomi da suke da laka da shi.



3443784

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha