Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na France 24cewa, wata mata ta fuskanci cin zarafi da duka a metro a birnin Marcelle ma kasar Faransa bayan da aka ganta da hijabin musulunci, indsa aka jikkata ta.
Bayanin ya ce bayan da matar ta samu kanta a a cikin jinni a kwace, an dauke ta zuwa wani asibiti domin ceto rayuwarta sakamakon duka da ta sha a hannun wasu yan kasar faransa masu kyamar musulmi.
Mata musulmi na fuskantar tsangwama a kasar faransa a lokiacin da aka gane cewa su musulmi ne ta hanyar saka hijabin muslunci tun bayan bayan kai harin da aka yi a kasar a makon da ya gabata.
Wannan cin zarafi da ake yi wa muslmi a kasar Faransa yana zuwa a daidai lokacin da adadinsu ya kai miliyan 8, wanda hakan ke nuni da cewa su ne na biyu a kasar bayan mabiya addinin kirista.
3454481