IQNA

Musulmi Shia Da Sunna Sun Gangami A gaban White House

22:59 - November 21, 2015
Lambar Labari: 3455353
Bangaren kasa da kasa, daruruwan musulmi sun gudanar da wani gangami a gaban fadar White House da ke birnin Washington na kasar Amurka, inda suka yi Allawadai da ta’addanci.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Fox5 ta bayar da rahoton cewa, musulmin sun fara ne da yin addu’a ga wadanda suka rasa rayukansu a Masar, Paris, Beirut da kuma Mali, haka nan kuma sun daga kwalaye da aka yi rubutu a kansu da ke yin Allawadai da ayyukan ta’addanci tare da nisanta kansu da addininsu daga irin wadannan ayyuka na dabbanci da kungiyoyi irin su ISIS ke yi da sunan jihadi.

Daruruwan musulmin sun gudanar da wannan gangami ne a gaban fadar White House da ke birnin Washington na kasar Amurka, inda suka yi Allawadai da ta’addanci, tare da yin Allawadai da tsangwamar da ake nuna musu sakamakon ayyukan da ‘yan ta’adda ke aikatawa.

Sayyid Ashraf daya daga cikin wadanda suka shirya wannan gangami ya bayyana cewa,a bin da suke yi yana dauke da sako ga dukkanin al’ummar Amurka kan cewa addinin muslunci addini na zaman lafiya tare da bil adama baki daya.

Kamar yadda shi ma Hassan Ahmad daya daga cikin jagororin muslumia  kasar ta Amurka ya bayyana cewa, ya zama wajibi a kawo karshen tsangwamar da ake nuna wa musulmi a wasu kasashen turai, wadanda ba su san haw aba balanta sauka, ya kara da cewa ya kamata a lura da cewa fiye da kashin casein da tara  cikin dari na mutanen da ‘yan ta’adda suka kashe musulmi ne.

3454963

Abubuwan Da Ya Shafa: amurka
captcha