IQNA

An Bude Bangaren nazarin Kur’ani Mai Tsarki A Jami’ar Nigeria

21:02 - November 25, 2015
Lambar Labari: 3457202
Bangaren kasa da kasa, an bude bangaren nazarin kur’ani mai tsarki a jami’ar jahar Yobe da ke tarayyar Najeriya.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na  «The Nation» cewa, an bude wannan bangaren nazari a jami’ar ta Yobe domin domin yin nazari kan sahihiyar fahimta ta kur’ani.

An gina wannan bangare bisa tsari na koyarwa wanda zai zama ya yi daidai da sauran cibiyoyin nazarin kur’ani na duniya musamman na kasashen musulmi.

A cewar Musa Alabe mataimakin shigaban jami’ar Yobe wannan bangare zai mayar da hankali wajen yin amfani da sahihiyar koyarwa ta kur’ani domin yaki da tunanin Boko Haram.

Alabe ya ce; akwai hanyoyi da yawa na yaki da matsalar Boko Haram haram da hakan ya hada da magance matsaloli na talaucia  tsakanin matasa, baya ga haka kuma akwai bababr hanya ta wayar da kai kan addini, domin kuwa kwai mutane da suka hardaace kur’ani mai tsarki, amma ba su san yadda za su amfanar da mutane da shi ba.

Ya ce sadoda haka za su yi amfani da wannan damar wajen hada mutane masu ilimin kur’ani domin su zama a sahun gaba wajen wayar da kan mutane kan hakikanin koyarwar kur’ani mai tsarki kan zaman lafiya.

Mataimakin shugaban jami’ar ta Yobe ya ce a halin yanzu suna da dalibai kimanin 50 zuwa 60 wadanda za a fara da su, kuma suna sa ran daga nan zuwa wani dan lokaci za su samu mutane fiye da dubu daya, kuma suna fatan sauran jami’oin arewacin najeriya za su yi koyi da wannan shiri.

Ya ce da farko za su fara da adadin dalibai kadan, domin su samu damar yin amfani da hakan wajen tabbatar da shirin ya yi nasarr da ake bukata domin kaiwa ga manufar da ake son cimmawa.

3456910

Abubuwan Da Ya Shafa: najeriya
captcha