Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar talabijin ta Alalam, wanda ya nakalto daga shafin Al-nashrah cewa, dukkanin labaran da ake yada kan cewa Sayyid Nasrullah ya tafi kasar Iraki boye basu da tushe balantana makama, kirkirace ta wasu kafofin yada labarai kawai.
Kafin wannn lokacin dai wasu kafofin yada labarai sun yi ta baza bayanin cewa Sayyid Hassan Nasrullah ya tafi kasar Irakia boye, domin halartar tarukan Arbaeen na wannan shekara.
3459727