Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar yada al’adun muslunci cewa, Musatafa Burujardi, Muhammad Asadi Muwahhad, shugaban ofishin yada al’adu na Iran a Tunisia, a lokacin ganawarsu da Usman Battikh da suka kai masa goron gayyata zuwa taron makon hadin kai ya gana da su.
Ministan ya ce ko shakka babu yada tsatsaran ra’ayi da ake yi da sunan addini, shi ne babban abin da ke haifar da tunin ta’addanci, wanda yake dibar dubban matasa daga cikin musulmi a halin yanzu kamar yadda kowa yake gani, wanda kuma hakan yana tattare da babban hadari ga duniyar musulmi baki daya.
Babbar manufar ganawar bangarorin biyu dai ita ce mika goron gayyata ga ministan harkokin addini na kasar ta Tunisia ne zwa babban taro na kasa da kasa kan hadin kan al’ummar musulmi wanda za agudanar nan ba da jimawa ba, inda kuma aka isar masa da sakon wakilin Jgora kan ayyukan Hajji Hojjatol Islam Ghadi Askar..
Bururjardi ya jaddada muhimmancin hadin kan al’ummar musulmi da kuma rawar da malamai suke takawa wannan bangare domin tabbatar da cewa an fuskanci hakikanin abin da ke ci ma duniyar muslmi tuwo a kwarya, maimakon bata lokaci kan wasu lamurra na gefe.
A nasa bangaren Usman Battikh ya nun adamuwa matuka dagane da kisan kiyashin da ak yi wa mahajjata a mIna a wannan shekara, tare da bayyana cewa hakan a bin ban takaici ne.
3460456