IQNA

Babu Tsatsauran Ra’ayi Da Tashin hankali A Cikin Addinin Ubangiji

23:44 - December 11, 2015
Lambar Labari: 3462162
Bangaren kasa da kasa, Gholam Ali Khoshrou jakadan jamhuriyar muslunci ta Iran a majalisar dinkin duniya ya gabatar da wani bayani na gwamnatin Iran a gaban majasar dangane da yaki da ta’addanci.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Press TV cewa, a jiya cewa Gholam Ali Khoshrou jakadan jamhuriyar muslunci ta Iran a majalisar dinkin duniya, ya gabatar da wani bayani da ke bayyana matsayin gwamnatin Iran a gaban majasar dangane da yaki da ta’addanci a wannan lokaci, wanda ake kisan bil adsama da sunan addinin muslunci.



Bayanin y ace jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gabatar da daftarin kuduri ga Majalisar Dinkin Duniya mai taken “Tsarkake duniya daga tashe-tashen hankula da tsaurin ra’ayi”.



A yammacin jiya Alhamis ne jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya Gholam Khushrou ya gabatar da taftarin kudurin ga babban zauren Majalisar Dinkin Duniya yana mai bayyana cewa.



Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta dauki matakin gabatar wannan daftarin kuduri ne ganin yadda kasashen duniya suka goyi bayan shawararta kan wajabcin daukan matakan kalubalantar matsalolin da suke janyo tsaurin ra’ayi da wuce gona da iri a duniya.



Jakadan na Iran ya jaddada cewa; Dukkanin addinan da suka zo daga wajen Allah Madaukaki babu wanda yake kira zuwa ga tsaurin ra’ayi da wuce gona da iri.



Yana mai gargadin cewa; Mummunan matakin nuna bambanci, kyamatar juna, zargin mabiya wasu addinai, babu wani tasirin da hakan zai yi banda karfafa tunanin tsaurin ra’ayi da ayyukan ta’addanci.



Daga karshe ya yi kira ga kasashen da suke daukar nauyin ayyukan ta’addanci a duniya da su kwana da sani cewa abin da suke yi ko badade ko ba jima zai dawo a kansu, kuma masu yin hakan a sansu aduniya, amma saboda rashin adalci da ke tafiyar da duniyar, an shiru an zura musu ido.



3462080

Abubuwan Da Ya Shafa: UN
captcha