IQNA

Samir Quntar Ya Yi Shahada A Wani Harin Isra’ila A Damascus / Hizbullah Ta Tabbatar

23:09 - December 20, 2015
Lambar Labari: 3467517
Bangaren kasa da kasa, a harin da jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ial suka kai da jijjifin safiyar yau a kusa da birnin Damascus na Syria babban kwamandan Hizbullah ya yi shahada.


Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tahar Press TV cewa, Samir Qantar yay i shahada daya daga cikin kwamandojin sojinta sakamakon wani harin ta'addanci da jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai masa a gidansa da ke yankin Jarmana, da ke kusa da birnin Damaskus, babban birnin kasar Siriyan.Kafafen watsa labaran kasar Labanon din sun bayyana cewar a safiyar yau Lahadi ne jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ilan suka kai hari gidan shahid Samir Qantar da ke garin Jaramana tare da fararen hula 10, dake kimanin kilomita 10 daga birnin Damaskus babban birnin kasar Siriyan; lamarin da yayi sanadiyyar shahadarsa da kuma wasu mutane goma 'yan kasar Siriya baya ga wadanda suka sami raunuka.Yayin da suke sanar da labarin shahadar, iyalansa ta bakin kanin Shahid Qantar din wato Bassam Quntar cikin wata sanarwa da ya rubuta a shafinsa na facebook ya sanar da shahadar wan nasa.A shekara ta 2008, yayin musayen fursunoni da kungiyar Hizbullah, ne Haramtacciyar kasar Isra'ila ta sako Samir Quntar daga gidan yari bayan ya shafe kimanin shekaru 29 a gidan yarin.Kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon ta tabatar da shadar Samir Qantar tare da wasu fararen hula da suke cikin ginin da aka kaiwa harin.Hizbullah ta bayyana wannan hari da cewa daya ne daga cikin ayyukan ta’addanci na aramtacciar kasar Ira’ila, kuma ba zai zama na karshe ba a kan masu gwagwarmaya.

A nasu bangaren kungiyoyi na gwagwarmaya sun bayyana wannan ta’addanci da cewa ba zai wuce haka nan ba tare da mayar da mataniya kan yahudawan sahyuniya, kuma hakan zai zama ba da jimawa ba.3467311Abubuwan Da Ya Shafa: lebanon
captcha