IQNA

Musulmi A Bristol Suna Taimakon Marassa Galihu

23:23 - December 26, 2015
Lambar Labari: 3469682
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci suna taimakama marassa abin hannun a lokacin idin kirsimatin Isa (AS) abirnin Bristol.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin Bristol Post cewa, Mabiya addinin muslunci a birnin Bristol na kasar Birtaniya suna taimakon marassa galihu da abinci da kuma wasu kayayyakin bukatar rayuwa, tare da taya su murnar kirsimati na haihuwar annabi Isa (AS)



Kamfanin dillanicn labaran Inqa ya habarta cewa ya nakalto daga shafin yada labarai na Bristol Post cewa, a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan kirsimati, mabiya addinin muslunci a birnin Bristol sun shagaltu da gudanar da ayyukan jin kai da taimaka marassa abin hannu.



Muhammad Sharif daya daga cikin wadanda suke gudanar da wannan aiki ya bayyana cewa, manufarsu ita ce yin taimako ga dan adam kamar yadda musulunci ya yi umarni.



Shi ma Abdulmalik limamin wani masallaci a birnin na Bristol ya bayyana cewa, abin takaici ne yadda aka bata sunan muslunci a tsakanin al'ummar kasar Birtaniya da ma sauran kasashen turai, sakamakon munanan ayyukan kisan gilla da 'yan ta'adda suke aikatawa da sunan addinin mulsunci.



Ya ce wannan ya sanya da dama daga cikin mutanen kasar suna yi wa muslunci wani mummunan kallo, a kan ya ce dole ne su fito su nana wa mutanen Birtaniya irin kyawawan dabiu da addinin muslunci yake koyar da mabiyansa, sabanin abin da suke zato.





3469170

Abubuwan Da Ya Shafa: Bristol
captcha