IQNA

Za A Buga Mushafin Masallacin Aqsa a Cikin Palastinu

23:27 - December 26, 2015
Lambar Labari: 3469684
Bangaren kasa da kasa, za a buga mushafin masallacin Aqsa a cikin palastinu nan ba da jimawa ba.


Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na aynar gizo na Almashriq cewa, Muhmud Alhabbas babban alkalin birnin quds cewa, nan ba da jimawa ba za a wallafa wani mushabi mai sunan mushafin Aqsa  acikin yankin na Palastinu.



Ya ci gaba da cewa a taron maulidin amnzon Alalh da aka gudanara  abirnin ramalallah tare da halartar shugaban Palastinawa Mahmud Abbas cewa, nan da wasu lokuta masu za a kaddamar da wannan mushafi.



Mahmud Alhabbash ya bayyana cewa a wannan shekara tarukan maulidin amnzo ya sha banban da sauran lokuta, domin kuwa ya zo dai lokacin da ake gudanar da bukuwan tunawa da haihuwar annabi Isa almasih (AS) a cikin duniya.



Shi ma a nasa bangaren minstan kula da harkokin addinin palastinu Isa Adis ya bayyana cewa za su ci gaba da kokarinsu na ganin an gudanar da wannan aiki na buga kur’anin, wanda zai zama shi ne na farko mai wannan suna.



Kur’anin dai zai kasance aikinsa baki daya an gudanar da shia  cikin palastinu, kama daga rubutunsa da kuma aikin tantance da duba shi, da kuma buga shi, wanda hakan zai zama wani aiki na musamman da mamalamn ku’ani na palastinu za su gudanar.

3469305

Abubuwan Da Ya Shafa: palastinu
captcha