Kamfanin dilalncin labaran iqn aya nakalto daga shafin yanar gizo na
tashar Ala’am cewa, rahotannin daga Nijeriya sun bayyana cewar dubun
dubatan 'yan kungiyar harkar Musulunci a kasar sun fito kan tituna da
dama daga cikin biranen kasa a yau Jumu'a don kiran mahukuntan Nijeriya
da su sako jagoran kungiyar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da suka kama a
ranar Litinin din da ta gabata.
Shafin harkar Musuluncin na internet
ya bayyana cewar an gudanar da irin wadannan jerin gwano da gangami ne a
garuruwa daban-daban na kasar da sauran birane inda masu jerin gwanon
wadanda suke dauke da hotunan Sheikh Ibrahim El-Zakzaky suka bukaci da a
sako musu shugabansu da ke tsare a hannun jami'an tsaron kasar.
Shafin ya kara da cewa an dai gama jerin gwanon lafiya ba tare da faruwar wani rikici ba.
Har
ya zuwa yanzu dai jami'an tsaron Nijeriyan suna ci gaba da tsare
shugaban kungiyar 'yan'uwa musulmin Sheikh Ibrahim El-Zakzaky a wani
wajen da ba a tantance ko ina ba ne, duk da cewa babban hafsan hafsoshin
sojojin kasa na Nijeriyan ya bayyana cewar tuni sun mika Sheik
El-Zakzakin ga hukumar da ta dace don gurfanar da shi a gaban kotun.
3470362