IQNA

Ya Kamata malam Sunnah Su Bayyana matsayin Kan kisan ‘Yan Shia

8:44 - January 03, 2016
Lambar Labari: 3480006
Bangaren kasa da kasa, harkar muslunci a Najeriya ta kirayi malaman sunna a kasar da su bayyana matsayinsu kan kisan gilla da sojojin najeriya suka yi yan shi’a a kasar.
Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto daga shafin yanar gizo na Shafaqana cewa, harkar muslunci a Najeriya a karkashin jagorancin sheikh Ibrahin Zakzaky ta soki kafofin yada labarai da shafukan yanar gizo na gwamnati a kasar kan boye gaskiyar abin da ya faru.
Kamar yadda kuma harkar ta kirayi malamai da masana a kasar da su bayyana matsayinsu kan kisan gilla da sojojin suka yi maimakon yin shiru ko gunaguni.
Bayanin ya ce wasu suna ta hankoron ganin sun bayyana lamarin da cewa wata kungiya ce kawai ta wasu tsiraru har ma suna kira da a haramta kungiyar Zakzaky alhali abin ake yi bai takaita ga yan shi’a ba kawai.
Akwai yan sunan da kiristoci da suke shigowa ana yin taruka da su domin kuwa suna ganin abin da ake bai ta kaita da wani bangare ba Magana ce ta musulunci kawai.
A kan haka ne a ranar Quds yan shi’a da yan sunna duk suna shiga wannan jerin gwano domin abin da ake yi ana kare palastinawa ne yan sunna, kamar yadda har kiristoci suna shiga, domin kuwa batu da ya shafi yan adamtaka.
3470655
captcha