Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta
cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta
Alalam cewa, taron ya samu halartar malamai da masa kimanin 700 daga
kasashe kimanin 60 na duniya wanda masana na jami’ar Almostafa (SAW)
suka shirya a Tehran.
An bude taron ne da bayanin Sheikh Naim Kasim mataimakin babban sakatae na kungiyar Hizbullah, wanda ya bayyana Ayatollah Isa kasima amatsayin malamia bin koyi ta fuskar iliminsa da kuma tsayin daka kan neman hakkokin al’ummarsa.
Ayatollah Isa Kasim na daga cikin manyan malamai da suke jagorantar yunkurin al’ummar kasar domin neman yanci daga mulkin zalunci na mulukiya a kasar ta hanyar lumana ba tare da tashin hankali ba.
Wannan taro dai ya zo nea daidai lokacin da ake gudanar da bababn taron makon hadin kai na duniya a karo na ashirin da tara, wanda masu bincike na jami’ar Almostafa suka dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Daga karshe an bayar da bababr kyauta ta jami’ar Almostafa ga Ayatollah Sheikh Isa Kasim, tare da bayyana shia matsayin malami abin koyi ga sauran malamai na kasashen musulmi da larabawa.