IQNA

Wasu Shugabannin Larabawa Tare Da Isra’ila Suna Hankoron ganin Bayan Shi’a

9:30 - January 03, 2016
Lambar Labari: 3480015
Bangaren kasa da kasa, Rasim Nafis daga cikin shugabannin yan shi’a a kasar Masar ya ce wasu shugabannin larabawa suna hada kai tare da Isra’ila domin ganin bayan yan shia musamamn Iran da Hizbullah.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Yaum Sabi cewa, Rasim Nafis ya rubuta wata makala a matsayinsa na daya daga cikin shugabannin yan shi’a a kasar Masar yana cewa, wasu shugabannin larabawa suna hada kai tare da Isra’ila domin cutar da yan shia musamamn Iran da Hizbullah da suka tsone musu ido.

Dangane da makircin da wadannan shugabanni da sarakunan larabawa suke kullawa ya bukaci taimakon bababn sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah.

Haka nan kuma wannan babban masani na kasar ya aike da wani sako zuwa Sayyid Muktada Sadr na kasar Iraki, yana mai sanar da cewa mabiya tafarkin iyalan gidan amnzo  a Masar zasu yi aiki da dukaknin nasihohin da ya yi musu.

Rasin Nafis ya kara da cewa matakin ma’aikatr kula da harkokin addini ta kasar Masar ta dauka na rufe masallacin Ra’asul Hussain a lokutan tarukan Tasu’a da Ashura bababn kure ne.

3471418

captcha