Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Financial Times cewa, David Cameron firayi ministan kasar Birtaniya ya dage tafiyarsa zuwa Riyadh sakamkon kisan da Saudiyya ta yi kan mutane da suka hada da Sheikh Nimr saboda dalilai na siyasa.
David Cameron ya dakatar da tafyar da ya shirya yi zuwa kasar ta Saudiyya ne shi ma kan batun cinikin makamai a tsakanin kasashen biyu.
Cameron ya dakatar da tafiyar ne sakamakon matsin lambar da ya fuskanta kan daga wasu 'yan majalisar dokokin Birtaniya da ma wasu jam'iyyun siyasa na kasar, bayan kisan da Saudiyya ta yi kan sheikh Nimr da kuma masu fafutukar kare hakkin bil adama a kasar saboda dalilai na siyasa.
Wani da rahoton yana cewa, ministan tattalin arzikin na kasar jamus ya bayyana cewa, daga cikin abubuwan da kasar za ta sake yin nazari kansa har da batun sayarwa kasar ta Saudiyya tankokin yaki wanda suka yi magana a kai.