Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alakhbar na kasar Mauritania cewa, Yahya Wuld Hadmain firayi ministan kasar Mauritaniya ya bayyana cewa sharadin da zai sanya asake bude makarantun kur’ani da aka rufe shi ne bayani kan hanyoyin samun kudinsu da suke tafiyar da harkokinsu.
Ya ci gaba da cewa dukkanin makamarntun da aka rufe a halin yanzu a cikin kasar Maurtaniya an yi hakan ne saboda rashin lasisi da wadannan makarantu ba su da shi, wanda kuma hakan a cewarsa ya sabawa doka.
Ya ci gaba da cewa a shirye suke su bude dukkanin makarantun da aka rufe matukar dai sun cika sharuddan da aka kafa a dokar kasar, saboda haka yana da kyau su mayar da hankali wajen cika sharuddan kafin a basu damar ci gaba da ayykan nasu.
Haka nan kuma Firayi ministan ya yi ishara da cewa wannan batu yana daga cikin abubuwan da za a tattauna a kan su a majalisa, kuma za a dauki dukkanin matakan da suka dace domin tabbar da cewa an yi tsari ga sha’anin karatun kur’ania kasar.
Dangane da batun sharadin samun bayani kan kudaden shiga na makarantun kuwa, ya ce wanann doka tana nan, domin kuwa babu yadda za a bar makarantu su zauna babu tsari kuma ba a san inda suke samun kudadensu an shiga ba, domin tabbatar da tsaron kasa.
http://iqna.ir/fa/news/3465712