Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Telegraph cewa, Roz Hamid musulma ‘yar shekaru 56 da haihiwa, an fitar da ita daga wurin Donald Trump a lokacin d yake gabatar da taron kamfe na neman zama dan takarar shugabacin kasar a garin Rock Hel na jahar Carolina ta arewa.
Ba7yanin ya ci gaba da cewa a lokacin Trump yake Magana a kan yang dun hijira na kasar Syria, ya yi maganganu da matar ba ta ji dadinsu ba, a lokacin ta yi yunkurin ta fita, amma kuma sai ta zauna, saboda haka aka fitar da ita daga wurin tare da yi mata cin fuska.
Da dam adaga cikin masu bin kadun abubuwan da suke wakana kan takarar wannan mutum dai suna ganin cewa baya kiyaye kaidoji nay an ta;ara, inda yakan ci zarafin musulmi hankalinsa kwance, ba tare da daukar wani mataki a kansa ba.
Yanzu hakan dai wasu daga cikin masu bin addinin muslunci da suke mara baya ga wannan dan takara suna janye masa tare da bayyana abin da yake ya sabawa dukkanin kaidoji da suka kamata.
Donald Trump dai ya kasance daya daga cikin masu kudi a kasar Amurka, wanda yake da girman kai da raina sauran mutanen kasar musamman ma dai marassa karfi, kafin daga bisani kuma kiyayyrsa ta bayyana akan musulmi kamar dai yadda ake gania halin yanzu a lokacin yawon kamfe da yake yi.
3465921