
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana jawabin da shugaban kasar China yayi dangane da wajibcin samar da wata kyakkyawar hanya ta fadada alaka da aiki tare tsakanin kasashen da suke bisa wannan tafarki a matsayin wani lamari da yayi daidai da hankali sannan kuma abin yarda, inda ya ce: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba mancewa da irin hadin kai da kyakkyawar alakar da kasar China ta nuna mata ba a zamanin da aka sanya mata takunkumi.
Ayatullah Khamenei ya bayyana ‘makamashi' a matsayin daya daga cikin abubuwa masu muhimmanci a wannan duniyar, don haka sai ya ce: Iran ita ce ‘yantacciyar kasa daya tilo a yankin nan da za a iya dogaro da ita a bangaren makamashi. Don kuwa sabanin sauran kasashen yankin, Iran ce kawai kasar da babu wani abin da ke tasiri cikin siyasarta ta makamashi in ba dalilai na cikin gidan ta ba.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da siyasar mulkin mallaka na wasu kasashe musamman ma dai Amurka da alaka ta yaudara da take yi da sauran kasashen duniya, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: Irin wannan yanayin ne ya sanya kasashe ma'abota ‘yancin kai suke bukatar karfafa alaka a tsakaninsu. Yarjejeniya da kuma alaka mai muhimmanci ta shekaru 25 tsakanin Iran da China sun ginu ne bisa wannan turbar. A saboda haka wajibi ne a yi dukkanin abin da za a iya wajen ganin an aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma a aikace.
Har ila yau kuma yayin da yake ishara da irin yadda dubi da kuma fatan kyautatuwar alaka tsakanin kasashen gabashi da ke tattare da al'ummar Iran, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: Koda wasa kasashen yammaci sun gaza wajen janyo hankulan al'ummar Iran zuwa gare su da kuma yarda da su.
Ayatullah Khamenei ya bayyana siyasar Amurka dangane da Iran da cewa ita ce siyasar da ta fi muni da kuma nuna kiyayya idan aka kwatanta ta da siyasar sauran kasashen yammaci, don haka sai ya ce: Irin wannan siyasa ta kiyayya ita ce ta sanya al'umma da kuma jami'an kasar Iran suke neman kulla da kasashen duniya ma'abota ‘yancin kai.
Har ila yau kuma yayin da yake ishara da maganar shugaban kasar China dangane da batun karfafa alaka ta tsaro tsakanin kasashen biyu, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewar: Abin bakin cikin shi ne cewa irin bakar siyasar kuskure ta kasashen yammaci haka nan kuma da irin gurguwar fahimtar da wasu suka yi wa Musulunci, hakan sun sanya wannan yanki namu fuskantar matsalar rashin tsaro, wanda wajibi ne a yi amfani da hikima da hada kai waje guda don fada da hakan.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana wasu kasashen wannan yankin a matsayin tushen bayyanar irin wadannan gurbatattun tunani inda ya ce: Su kuma kasashen yammaci maimakon su yi fada da tushe na asali na wannan tunani da kuma kungiyoyin ta'addanci, sai suka koma kan musulman da suke Turai da Amurka da kuma ci gaba da matsa musu lamba, alhali kuwa wadannan kungiyoyi na ta'addanci sun yi hannun riga da ingantacciyar akida kuma tunani na Musulunci.
Har ila yau kuma yayin da yake ishara da dagewar da Amurkawa da kasashen yammaci suka yi wajen amfani da kalmar "Gwamnatin Musulunci" a kan wasu daga cikin kungiyoyin ‘yan ta'adda, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Hakan cin mutumci ne ga musulmai, wanda maimakon magance matsalar hakan yana share fagen karfafa wadannan kungiyoyi ne ko da kuwa ba kai tsaye ba.
Jagoran ya bayyana ikirarin Amurkawa na kafa ‘Hadakar Fada da Ta'addanci' a matsayin wata yaudara kawai inda ya ce: Wannan ita ce siyasar Amurka cikin dukkanin lamurra. Babu wani lokaci da suke nuna gaskiya cikin mu'amalarsu.
Daga karshe Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana fatan cewa: sakamakon tattaunawa da yarjejeniyoyin da aka cimma yayin wannan ziyarar za su kasance masu amfani ga dukkanin kasashe biyun.
Shi ma a nasa bangaren shugaban kasar China Xi Jinping, wanda shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ke wa jagoranci ya bayyana tsananin farin cikinsa da wannan ziyarar da ya kawo kasar Iran da kuma godiya ga irin tarbar da aka yi masa yana mai cewa hakan ta samo asali ne sakamakon irin tsohuwar alaka da abokantaka da ke tsakanin kasashe biyun ne. Har ila yau shugaban kasar China ya bayyana cewar: wajibi ne a ci gaba da karfafa alakar da ke tsakanin kasashen Iran da China bisa tushen amfanin da kowa zai samu.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da dadaddiyar hanyar sadarwa da alaka tsakanin Iran da China, shugaban kasar China ya bayyana wannan hanyar a matsayin wata alama ta ‘sulhu, ci gaba da kuma musayen abokantaka' a tsakanin kasashen biyu, inda ya ce: Ta hanyar aiki tare, kasashen da suke kan wannan hanyar za su iya kare manufofinsu daga barazanar da Amurkawa suke musu a fagen tattalin arzikinsu, sannan kuma su kai ga isa ga manufofinsu.
Mr. Xi Jinping ya ci gaba da cewa: Wasu daga cikin manyan kasashen duniya suna kokarin tabbatar da siyasar nan ta neman tsokana ta cewa "ko dai kana tare da mu ko kuma kana tare da makiyanmu", to amma irin sabon ci gaban tattalin arziki da ake da shi a halin yanzu ya kwace irin wannan karfi da suka takaita shi ga kawukansu daga hannunsu da kuma share fagen aiki tare tsakanin kasashe ma'abota ‘yancin kai.
Shugaban kasar China ya bayyana irin goyon bayan da kasarsa ta ba wa Iran dangane da shirin nukiliyanta da kuma irin goyon bayan da Iran take ba wa siyasar tabbatar da kasar China guda kuma hadaddiya a matsayin alamar da ke tabbatar da ‘yantacciyar siyasar kasashen biyu da kuma kare manufofin juna inda ya ce: Mu dai muna fatan ganin an samu ci gaba, don haka a shirye muke, kamar yadda muka kasance tare da Iran a zamanin takunkumi, bayan dage wadannan takunkumin ma za mu ci gaba da fadada alakarmu a dukkanin fagage.
Mr Xi Jinping ya ci gaba da cewa: Tattalin arzikin China da Iran masu taimakawa junane. Don haka a yayin wannan ziyarar ma mun cimma yarjejeniya aiki tare ta shekaru 25. A shirye muke mu ci gaba da fadada alakarmu da Iran a bangarorin al'adu, ilimi, fasaha, soji da kuma tsaro.
Shugaban kasar China ya bayyana samar da wata hanya ta karfafa alaka ta tsaro tsakanin Iran da China don fada da ta'addanci da kuma sauran batutuwa masu sarkakiya da suka shafi yankin nan a matsayin wani lamari da ya zamo wajibi.
Mr. Xi Jinping ya bayyana jawabin da Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi a matsayin wani jawabi da ke cike da hikima da kuma hangen nesa, don haka sai ya ce: Gwamnati da kuma al'ummar kasar China suna maka kallo na girmamawa. Don haka muna fatan kamar yadda ka saba yi, za ka ci gaba da taimakawa wajen karfafa alakar da ke tsakanin kasashe biyun.