
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya
habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sahra Magribiyyah
cewa, cibiyar kula da ayyukan addini ta kasar ce za ta dauki nauyin shirya
wannan taro.
Kwamitin da zai jagoranci alkalancin
wannan gasa zai kunshi mutane da suka hada da Hajir Busaq, fitatten makarancin
kur’ani da ya zo na daya akasar, da kuma
sheikh Said Muslim gami da wasu daga cikin fitattun makaranta da suka
shhara akasar, su ne za su kasance
alkalan gasar.
An sanar da cewa fiye da makaranta
400 za su halarci wannan gasa daga sassa na kasar Morocco.
Kamar yadda kuma aka sanar da cewa
bayan kammala wannan taron gasa za abayar da kyauta ta musamman ga wadanda suka
nuna kwazo, kuma kyautar za ta zama da kudi ce lakadan, kamar yadda kuma za a
gayyaci wasu fitattun mutane a kasar wadanda za su gabatar da kyautukan.
A karshen wannan gasa za a girmama
Allamah Muhammad Alkintawi fitaccen malamin addinin muslnci d ya bayar da
gudunmawa a dukkanin bangarori na ilimin kur’ania kasar a kasar.