
Kamfanin
dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar
gizo na Qaf cewa, cibiyar Imam Hussain (AS) ce ta dauki nauyin shirya gudanar
da wannan zaman taro.
Wannan taro
an gudanar da shi tare da hadin gwiwa da kungiyar dalibai na Afirka, wanda aka
gudanar a babban dakin taro na Warisul anbiya a birnin Qom tare da jagoranci Ma’aruf
Abdulmajid daga kasar Masar.
Haji Musa
Fal daga kasar Senegal tare da karamin jakadan kasar a Iran sun gabatar da wasu
daga cikin ayyukan kur’ani da aka rubuta
akasar a wajen wannan taro.
Ya ce tun
bayan da muslunci ya shiga nahiyar Afirka, an bayar da muhimmanci matuka wajen
gudanar da ayyuka da suska shafi kur’ani, ta hanyar bude makarantu da wuraren
nazari.
Ja’afar tarawure
mai bincike daga kasar Mali ya gabatar da jawabinsa kan muhimman ayyukan da
suka gudanar a kasar Mali a bangaren kur’ani, kamar su ma Sheikh Ibrahim daga
Senegal da sheikh Ismail Bellam daga Burkina Faso, Ali Ahmad ba Mauritaniya,
Hamid jalo Senegal, Ibrahim Muhammad daga Najeriya.
Wannan
cibiya da ke kula da irin wadannan ayyuka da suka shafi kur’ani da ke birnin
Qom, takan shirya taruka makamantan wannan, inda dalibai daga sassa na kasashen
Afirka da ke karatu da wadanda suke waje sukan halarta.