IQNA

An Fara Rijistar Sunayen Masu Gasar Kur’ani A Talabijin A kasar Algeriya

16:47 - February 02, 2016
Lambar Labari: 3480102
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki da ake gudanarwa kai tsaye ta hanyar talabijin a kasar Algeriya mai taken Mizamir Dawud wadda a wannan karon za a mayar da hankali kan surat Wadduha.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na echoroukonline.com cewa, wannan gasa za a gudanar da ita ne karkashin shekaru 15 na matasa masu halarta.

Bayanin ya ci gaba da cewa bisa la’akari da cewa an dauki tsawon shekaru ana gudanar da wanann gasa, a wannan karon lamarin zai dauki sabon salo.

Daga cikin abubuwan da za a gudanar kuwa har da jin sharhi da bayanin wasu ayoyi na musamman ko surori, baya ga karatun kur’ani mai tsarki da ya shafi kira’a zalla.

Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan shiri dai tashar talabijin ta Al-shuruq ce dai take daukar nauyinssa  akowace shekara, inda matasa yan kasa da shekaru 15 ke gabatar da karatu.

Haka nan kuma a wannan karo baya ga abubuwan da aka kara a cikin gasar, za a ware bangare kuma domin amsa tambayoyi kan kaidojin karatun kur’ani mai tsarki.

Wanann gasa dai tana samun karbuwa matuka a tasaknin al’ummar kasar, inda daruruwan yara kan rijistar sunayensu domin shiga a ciki, inda kuma iyayen yara kan bi kadun lamarin matuka domin ganin yaransu sun samu shiga.

Daga karshe dai akan bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka nuna kwazo a gasar a dukkanin bangarori, da hakan ya hada da kyautuka na kudi da kuma wasu kayayyaki masu kima gami da littafai.

3472196

captcha