IQNA

16:48 - February 08, 2016
Lambar Labari: 3480121
Bangaren kasa da kasa, Donald Trump dan takarar shugabancin kasar Amurka karkashin inuwar jam’iyyar Republican ya bayyana cewa mabiya addinin muslunci da dama a kasar suna sonsa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Daily Express cewa, Donald Trump dan takarar shugabancin kasar Amurka da ya yi kalaman batunci ga musulmi, ya bayyana cewa a cikin aboknsa 20 daga cikinsu musulmi ne.

A lokacin da yake amsa tambayoyin jaridar Daily Telegram, kan cewa shin idan ya lashe zabe zai kare hakkokin musulmi kuwa? Sai ya ce na gaya muku ni kai na inda abokai muuslmi guda 20 wadanda suke matukar kauna ta, amma yaki ya bayyana koda sunan daya daga cikinsu.

Kafin wannan lokacin dai Trump ya kasance a sahun gaba wajen nuna kiyayay matuka ga mabiya addinin musluncia  cikin kasar ta Amurka, musamman ma dai bakin haure wadanda suka yi hijira daga wasu kasashe zuwa kasar tasu, wanda hakan ya fuskanci kakakusar suka daga al’ummar kasar.

3473783

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: