IQNA

Ishara kur’ani daga Jagora:

Jamhuriyar Musulunci Da Zabe Na Gasgata Ayar (In Kun Taimaki Allah Zai Taimake Ku)

21:55 - February 09, 2016
Lambar Labari: 3480123
Bangaren siyasa, Aya ta 7 daga surat Muhammad (SAW) “In Kun Taimaki Allah Zai Taimake Ku “ na gasgata tsarin jamhuriyar muslunci da kumazabe a cikinta, kamar yadda jagora a jiya ya bayyana a lokacin da ya gana da manyan kwamandojin rundunar sojin sama ta kasar Iran.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na ofishin jagora cewa, a safiyar Litinin ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da kwamandoji da wasu daga cikin jami'an sojin sama na Jamhuriyar Musulunci ta Iran inda ya bayyana ranar 22 ga watan Bahman (ranar da aka sami nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran) da kuma zabubbukan da za a gudanar a kasar Iran din a nan gaba kadan a matsayin wasu ranakun idi guda biyu masu amfani ga al'ummar Iran. Haka nan kuma yayin da yake jaddada muhimmancin fitowar al'umma a jerin gwanon ranar 22 ga watan na wannan shekarar ya bayyana cewar: Fitowar mutane yayin zaben ranar 17 ga watan Esfand wani lamari ne da zai kara tabbatar da daukaka da kuma karfin Iran da kuma wannan tsari na Musulunci sannan da kuma yi masa lamuni budu da kari kuma kan hana makiya cimma manufofinsu.

Haka nan kuma yayin da yake jinjinawa irin fitowar da al'ummar Iran suke yi a wajen bikin murnar ranar 22 ga watan Bahman ta kowace shekara, Jagoran ya bayyana cewar: Fitowar da mutane suke yi a yayin jerin gwanon ranar 22 ga watan Bahman tsawon shekaru 37 din da suka gabata, wata fitowa da kasantuwa ce ta jiki tare da irada da azama da so da kauna. A bana ma da yardar Allah fitowar da mutane za su yi za ta kasance wata fitowa ta gaba daya wacce kuma za ta kasance mai bada wa makiya kasa a ido da kuma sanya su yanke kauna.

Ayatullah Khamenei ya bayyana ci gaba da gudanar da bukukuwan ranar 22 ga watan Bahman a matsayin sabunta bukukuwan idin nasarar juyin juya halin Musulunci wanda ba kasafai ake samun irinsa a sauran kasashen duniya ba. Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Tun farkon nasarar juyin juya halin Musulunci har zuwa yau, cikin kowane irin yanayi da aka samu kai ciki kuwa har har da lokutan tsananin gaske, amma al'ummar Iran sun kasance masu fitowa don gudanar da wadannan bukukuwa na ranar 22 ga watan Bahman.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Wani adadi mai yawan gaske na wadanda suke fitowa jerin gwanon ranar 22 ga watan Bahman na shekarun baya-bayan nan, saboda yanayin shekarunsu, ba su shaidi ranakun juyin juya halin Musulunci da kuma ranar 22 ga watan Bahman na shekarar 1357 (1979) ba. Irin ci gaban wannan silsila ta al'umma maras karshe wata alama ce da ke nuni da irin karfin da wannan juyi yake da shi.

Haka nan kuma yayin da yake bayyana cewar bai kamata a mance da irin abubuwan da suka faru a baya ba, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewar: Wajibi ne a ci gaba da raya hakikanin abubuwan da suka faru yayin juyin nan da tabbatar da su a cikin kwakwalan mutane. Don kuwa juyin juya halin yana tsakiyar hanyarsa ne. A saboda haka don isa ga manufofinsa da kuma karfafa tushensa yana bukatar ci gaba da kiyaye manufofinsa na asali.

Ayatullah Khamenei ya bayyana kafa al'umma musulma ma'abociyar ilimi, adalci, kyawawan halaye, daukaka da ci gaba a matsayin babbar manufar tsarin Musulunci inda ya ce: babbar manufar makiya ita ce sanya a mance da wannan babbar manufa wanda daga karshe zai kai ga sauya wannan tsari na Jamhuriyar Musulunci.

Haka nan kuma yayin da yake bayyana cewar babbar manufar makiya ita ce sauya irin wannan ruhi da yanayi na juyin juya hali da ke tattare da tsarin Jamhuriyar Musulunci, Jagoran ya bayyana cewar: Dukkanin kokarin sansanonin makiya da masu fatan sharri ga wannan tsari na Musulunci shi ne ganin sun kawar da Jamhuriyar Musulunci daga ci gaba da tafiyar da take yi wajen isa ga manufofinta na daukaka da kuma samun karfi sannan da kuma sake dawo da iko da mulkin ‘yan kasashen waje a kasar Iran.

Haka nan kuma yayin da yake kore yiyuwar kaddamar da yaki na makami a kan Iran a irin wannan yanayi da ake ciki a halin yanzu a duniya duk kuwa da cewa ba za a iya kore hakan gaba daya ba, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: A yau ne babban makamin da makiya suke amfani da shi wajen fada da tsarin Musulunci na Iran shi ne makamin lalata al'adu da kyakkyawar alakar da ke tsakanin mutane da wannan tsarin don kwace musu abin da ke tabbatar musu da karfinsu.

Jagoran ya bayyana kwace wa wata al'umma tushen karfinta a matsayin wani lamari ne da nuni da tilasta mata mika kai don haka sai ya ce: Matukar da al'ummar ta yi rauni, to babu bukatar amfani da makami wajen fada da ita.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewar: Hanya guda ta fada da irin wannan yanayi, ita ce kiyaye tunani da koyarwar juyin juya hali cikin ayyuka, halaye, matsaya da kuma dokoki.

A ci gaba da jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana zabe a matsayin wani lamari da ke kara karfi da sabun numfashi cikin zukatan al'ummar Iran yana mai cewa: A kokarinsu na amfani da hakkin da suke da shi, sannan kuma a daidai lokacin da aka tsara al'ummar (Iran) su kan shigo fage don daukar matsaya dangane da jami'an da suka zaba a baya, shin waye daga cikinsu zai ci gaba da sannan wane ne zai kauce.

Jagoran ya bayyana zabubbukan da ake gudanarwa a matsayin wani abu da ke sabunta irin karfin da al'ummar Iran suke da shi kana kuma sake yin mubaya'a ga manufofin juyin juya halin Musulunci don haka sai ya ce: Babban dalilin da ya sanya yake ci gaba da jaddada wajibcin fitowar mutane yayin zabe shi ne cewa fitowar mutane kwansu da kwarkwatansu yayin zaben ya kan kara wa kasar nan da kuma wannan tsari (na Musulunci) karfi da daukaka ne da kuma ba shi kariya. A saboda haka fitowa kada kuri'ar wani farali ne a wuyan dukkanin al'umma.

Ayatullah Khamenei ya bayyana kokarin haifar da gibi da baraka tsakanin al'umma da kuma gwamnati a matsayin daya daga cikin manyan kuma manufofi na koda yaushe na makiya musamman Amurka, don haka sai ya ce: Fitowar al'umma a yayin zabe da kuma sake tabbatar da alakar da ke tsakanin mutane da gwamnati tana nufin taimakon Jamhuriyar Musulunci da kuma hana makiya cimma wannan manufa ta su. Sannan kuma bisa alkawarin Allah, wannan fitowar tana tare da taimako irin na Ubangiji.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da makirce makircen da makiya suka dinga kullawa tun farko farkon nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran ciki kuwa har da shirin su na raba Iran, juyin mulkin soji, kallafaffen yaki na shekaru 8 da kuma takunkumi kala kala da suka dinga sanya wa Iran, Jagoran ya bayyana cewar: Duk fada da dukkanin wadannan makirce-makirce al'ummar sun fito wajen taimakon tsarin Musulunci, shi ma a nasa bangaren Allah Madaukakin Sarki ya tabbatar wa Jamhuriyar Musulunci da kuma al'ummar Iran suka zamanto wani karfi a wannan yankin, a wasu wajajen ma suka zamanto masu tasiri a fagage daban-daban na duniya.

Yayin da yake rufe wannan bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi al'ummar Iran da cewa: Daukaka da samu karfi na kasa da kuma al'ummar nan suna cikin aiki da nauyi na juyi da ke wuyanmu ne, wanda fitowa yayin zabe yana daga cikin irin wadannan nauyi masu muhimmanci.

A ci gaba da jawabin nasa dangane da batun zaben, Ayatullah Khamenei yayi ishara da wasu maganganu na kuskure wadanda ba su dace da wasu suke ta yi cikin ‘yan kwanakin nan da nufin kashe gwiwan mutane da sanya musu shakku cikin zukatansu inda ya ce: Wadannan maganganu ba wai kawai saboda siyasa ake yin su ba, akwai wata manufa da ta sa ake yinsu. Wanda a halin yanzu ba na son in yi magana kansu.

Haka nan kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi jami'an kasar ta Iran da su yi la'akari da wasu lamurra da suke da muhimmanci cikin lamarin da ya shafi zaben inda ya ce: Cikin ikon Allah jami'an gwamnati suna ci gaba da ayyukan da suka hau kansu, to amma wajibi ne su yi taka tsantsan wajen ganin ba su fada tarkon irin rikice rikice na ranakun zabe da zai hana su ayyukansu masu muhimmanci ba ciki kuwa har da batun kyautata tattalin arziki.

Ayatullah Khamenei ya bayyana zabe a matsayin wani lamari mai tsananin muhimmanci, inda ya ce: Lamarin zabe, duk kuwa da muhimmancin da yake da shi, amma wani lamari ne na wani lokaci, to amma lamurran da suke da muhimmanci bayan sa shi ne manyan batutuwa na kasa ciki kuwa har da batun karfafa tattalin arziki.

Har ila yau yayin da yake sake ishara da irin karfi na mutane masana kuma da kari kan albarkatun kasa da Iran take da shi, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi jami'an gwamnatin da cewa: Ta hanyar dogaro da wannan gagarumin jari maras tamka da ake da shi, ku yi kokari wajen gina tattalin arzikin kasar nan ta yadda makiya ba za su sake tunani amfani da matsin lamba na tattalin arziki wajen cimma manufofinsu a kan al'ummar Iran ba.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Yana da kyau jami'an gwamnati su kama hanyar karfafa masana'antu da abubuwan da ake samarwa a cikin gida da kuma bangaren aikin noma da magance matsalar koma bayan tattalin arziki da ciyar da kasar nan gaba don ala tilas makiya su fahimci cewa takunkumin tattalin arziki dai ya zama aikin baban giwa.

Haka nan yayin da yake ishara da jawabin shekaru 12 da suka gabata da yayi, Ayatullah Khamenei ya sake jaddada wa jami'an gwamnatin wajibcin karfafa tattalin arzikin kasa inda ya ce: matukar aka cimma wannan manufar, to kuwa za a sami hanyar da ta dace ta magance matsalar rashin aikin matasa, rashin aikin yi da sauran matsalolin da ake fama da su.

Wani batu na daban mai muhimmanci da Jagoran yayi ishara da shi, shi ne kula da kuma sanya ido a koda yaushe kan tarkon da makiya suka dana wajen cimma manufofinsu inda ya ce: Mutane ba za su taba jinjinawa mutanen da suka gafala daga makirce makircen makiyansu ba.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Makiya za su sake muku fuska, kuma za ku sake musu, to amma wajibi ne ku sanya ido dangane da yaudara da makircin da ke karkashin wannan sakin fuska na makiyan.

Ayatullah Khamenei ya jaddada cewar: wajibi ne a fahimci makircin makiya cikin batutuwa da suka shafi tsaro, rayuwar al'umma, al'adu, matasa da sauran matsaloli na zamantakewa don haka a tsara hanyoyi da dokokin da za su yi fada da hakan.

A saboda haka ne sai Jagoran ya kirayi jami'an gwamnatin da su kara yin taka tsantsan dangane da makirce-makircen makiyan yana mai cewa: Amurkawa sun gaza wajen ba wa al'ummomin duniya amsar tambayoyin da suke da shi kan dalilin da ya sanya suke goyon bayan masu aikata irin wannan danyen aiki na zalunci a kan al'ummar Yemen, sannan kuma suna ci gaba da goyon bayan mutanen da suke aikata ta'addanci irin ta gwamnati wajen kashe mutanen da ba su ci ba su sha ba a kasar Yemen.

Ayatullah Khamenei yayi watsi da ikirarin Amurkawa na kare hakkokin bil'adama da kuma tsarin demokradiyya a duniya inda ya ce: wadannan mutane suna ci gaba da goyon bayan gwamnatin sahyoniyawa mai kashe kananan yara da kuma sauran kawayensu wadanda ba su san komai kashin ma'anar zabe ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Wautar masu mulkin Amurka ta kai matsayin da su kan aikata mafi munin aiki amma kuma su juyo suna muku murmushi da sakin fuska. Ashe bai kamata a yi taka tsantsan da sanya ido sosai a kan irin wannan makiyin ba?

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Cikin taimakon Allah al'ummar mu sun fahimci wadannan makiyan, kuma ya zuwa yanzu gagarumin yunkurin al'ummarmu ya dushe wannan makirci na makiya mayaudara da hana su cimma manufofinsu, insha Allah a nan gaba ma haka lamarin zai kasance.

Tun a farkon jawabin nasa dai Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da mubaya'ar da sojojin sama na Iran suka yi wa marigayi Imam Khumaini (r.a) a ranar 19 ga watan Bahman 1379 (8, Fabrairun 1979) a matsayin wani lamari mai muhimmanci da kuma tasirin gaske inda ya ce: Abin da sojojin sama suka yi a ranar 19 ga watan Bahman na shiga cikin al'umma lamari ne da ya sauya yanayin kasar Iran wanda kuma ba tare da bata lokaci ba al'umma suka yi na'am da hakan. Hakan kuwa lamari ne da ke nuni da cewa kusatar mutane wani lamari ne da zai janyo goyon baya da kuma taimakawarsu.

Ayatullah Khamenei ya bayyana ayyukan sojojin saman na Iran tsawon shekaru 37 din da suka gabata da cewa wani aiki ne mai kyaun gaske inda ya ce: A halin yanzu ma dai sojojin saman sun kasance wasu gungun mutane masu karfi da tsayin daka wadanda kuma suke tare da mutane. A saboda haka wajibi ne a kullum a ci gaba da karfafa irin wannan alaka da ake da ita.

Kafin jawabin Jagoran dai sai da babban hafsan hafsoshin sojin sama na Iran din Vice Admiral Shah Safi ya gabatar da jawabinsa inda yayin da yake taya murnar zagayowar ranar 19 ga watan Bahman ya sake jaddada shirin da sojojin saman suke da shi wajen kasar kasar Iran daga dukkanin wata barazana ta makiya.

3474170

captcha