
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Manama Post cewa, kungiyoyin kare hakkinbil adama na ciki da wajen kasar Bahrain, sun kirayi masarautar kasar da ta daina takura ma mutane saboda suna bayyana albarkacin bakinsu kana bin da ke faruwa a kasarsu.
Bayanin ya ci gaba da cewa mutane suna da hakkin su fito su gudanar da taruka ko zanga-zanga domin bayyana ra'ayinsu da mahangarsu kan wani abu da yake faruwa acikin kasarsu, kuma takura musu kan haka take hakkin bil adama ne.
Suka cea cikin shekaru 5 da suka gabata ya zuwa yanzu, an tafka ayyuka na cin zarafin dan adam da keta huruminsa akasar Bahrain a karkashin masarautar kasar wadda ke bin tsarin kama karya na mulukiya.
Shi ma a nasa bangaren Yusuf Almahafah daya daga cikin masu rajin kare hakkokin bil dama akasar ya bayyana abin da yake faruwa da cewa abin yin Allawadai matuka.
Ya ce a cikin watanni 4 na karshen sheakara ta 2015 an kame mutane 400, kusan kasha 76 cikin dari an kame sub a tare da hakkinsu ba, sadomin dalilai na siyasa.
Shi ma a nasa bangaren Ahamd alwadai daya daga cikin masu rajin kare hakkokin bil adama kafa dimukradiyya a kasar ya bayyana cewa, maimakon mahukuntan kasar su saurari jama'a su zauna da su, sai suka gwammace yin amfani da karfi da kisa kan fararen hula.
Hayyu Ali babban daraktan zartarwa na cibiyar kare dimokradiyya kasar Bahrain ya bayyana cewa, bas u taba daina fadin gaskiya da kuma yin kira da a kare hakkokin jama'a marassa kariya akasar ba.