IQNA

An Fara Aiwatar Da Shirin Raba Kwafin Kur’ani Dubu 130 A Mauriyaniya

22:05 - February 19, 2016
Lambar Labari: 3480153
Bangaren kasa da kasa, an fara aiwatar da wani shiri n araba kwafin kur’ani dubu 130 a kasar Mauritaniya a wasu cibiyoyin addini a kasar gani da na kur’ani.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-siraj cewa, wannan shiri an fara aiwatar da shi kamar yadda aka shirya, daga cikin kwafin kur’anan dubu 50 an rubuta su ne bisaruwaya ta warsh, sai kuma dubu 30 da kira’ar Qalun, sai kuma sauran dubu 50 din kuma bisa kira’oi daban-daban.

Sheikh Umar Alfath shugaban cibiyar ayyukan alkhairi ta Ta’wun ya kafa wani kwamiti wanda zai dauki nauyin gudanar da wannans hiri kamar yadda aka tsara tun daga farko,a dukkanin cibiyoyin da za a rarraba su, da su hada da dakunan karatu.

Ya kara da cewa ya zuwa yanz cibiyoyi guda 45 ne wannan shiri zai shafa, da suka hada da cibiyoyi na yada al’adun muslunci, da kuma dakunan karatu na kur’ani, gami da wasu cibiyoyin wadanda su ma na addiniantu da suke horar da dalibai karatun kr’ani wasu daga cikinsu shirin zai hada har da su.

Wani mutum dan kasar Bahrain mai suna Abdulgaffar Abdulrahim Al-kuhji shi ne ya dauki nauyin gudanar da wannan aiki na lkhairi, kamar yadda ya saba yia wasu kasashe.

3476692

captcha