
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jagora cewa, a safiyar Laraba ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da dubun dubatan mutanen garin garin Najafabad inda a jawabi mai muhimmanci da yayi, ya yi karin haske kan kalmomin "masu sassaucin ra'ayi da masu tsaurin ra'ayi", kamar yadda kuma ya kirayi dukkanin al'ummar Iran musamman jami'ai da ‘yan siyasa da su yi taka tsantsan dangane da makirce-makircen makiya na haifar da rarrabuwan kai na karya a yayin zaben inda ya ce: Duk wadanda suke fatan ganin daukakar kasar Musulunci ta Iran, to wajibi ne su fito yayin wannan zaben. Lalle a ranar 7 ga watan Esfand duniya za ta ga yadda al'uummar Iran zasu fito kwansu da kwarkwatansu wajen kada kuri'unsu.
Haka nan kuma yayin da yake magana kan ranakun shahadar Nana Fatima al-Zahra, amincin Allah ya tabbata a gare ta, Ayatullah Khamenei yayi ishara da zabubbuka guda biyu masu matukar muhimmanci na majalisar shawarar Musulunci da majalisar kwararru ta jagoranci da za a gudanar ranar Juma'a mai zuwa inda yace: Muhimmancin asalin zabe a kasar (Iran) ba wai kawai ya takaita ga kada kuri'a ba ne, face dai zabe yana nufin sadaukar da kai ne wajen tinkarar makiya, bayan nau'oi daban-daban na matsin lamba da takunkumi na zalunci da bakaken farfagandoji.
Jagoran ya bayyana fitowar al'umma yayin zaben a matsayin lamarin da zai sake tabbatar da girma da daukakar juyin juya halin Musulunci a idon duniya, inda ya ce: Baya ga bayyanar da karfi, azama da tsayin dakan al'umma, har ila yau zabe wani lamari ne da ke nuni sadaukarwa, jaruntakar wata al'umma mai girma wajen tinkarar bakaken manufofin (makiya).
Bayan bayanin muhimmancin fitowar mutanen da suka cancanci kada kuri'unsu yayin zaben, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da bayanin makirce-makircen makiya tsawon shekaru 37 na nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran inda ya ce: ‘Inkari da karyata zaben da ake gudanarwa a Iran", "Kokari wajen hana mutane fitowa zabe ko kuma rage yawan fitowar" da kuma "Nuna rashin fa'idar fitowa yayin zaben saboda tun da jimawa an san yadda sakamakon zaben zai kasance" wasu ne daga cikin farfagandar da makiya suke yi tsawon shekarun da suka gabata da nufin kashe gwiwan mutane wajen fitowa zaben. A wasu lokuta ma jami'an Amurka a fili suke fadin hakan.
Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar a halin yanzu dai Amurkawa sun fahimci cewa fitowa fili suna fadin hakan wani lamari ne da ke sanya mutane fitowa zaben ma, don haka sai ya ce: A saboda haka ne Amurkawa suka gum da bakinsu yayin wannan zaben, to amma ‘yan mashin shatansu suna nan suna ta fama da kulla sabbin makirce-makirce ta hanyoyi mabambanta.
Dangane da wadannan sabbin makirce-makirce kuwa, Jagoran cewa yayi: Makircin da masu bakar aniya kan al'ummar Iran suka kulla wa wannan zaben, shi ne samar da wasu kungiyoyi biyu na karya don raba kan al'ummar Iran yayin zaben.
Har ila yau yayin da yake bayyana cewa yanayin zabe, tamkar duk wata gasa, akwai mai nasara da wanda zai fadi, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Wannan nasara ko rashin nasara a yayin zabe ba wai yana nufin raba kan al'umma da samar da bangarori biyu cikin al'umma da kuma haifar da yanayi na kiyayya da gaba a tsakaninsu ba ne. magana kan samuwar wadannan kungiyoyi biyu a Iran, wata karya ce kawai.
Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar kungiyoyi biyu na hakika da ake da su a Iran su ne ‘masu riko da juyin juya halin Musulunci da koyarwar marigayi Imam Khumaini (r.a)" da "sansanin ma'abota girman kai da masu ra'ayi irin na su" inda ya ce: Tabbas a tsakanin wadannan kungiyoyi biyu, kungiyar al'ummar Iran ita ce ‘kungiya mai riko da juyin juya halin Musulunci da koyarwar marigayi Imam Khumaini (r.a) da tafarkinsa".
Jagoran ya bayyana cewar: Wannan batu na kungiyoyi biyu ya samo asali ne daga kasashen waje, to amma abin bakin cikin shi ne cewa a wasu lokuta ma a kan sami wasu a cikin gida da suke nanata irin wannan maganar.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana batun da wasu suke yadawa na ‘majalisa ‘yar gwamnati' da kuma ‘majalisa mai adawa da gwamnati' a matsayin daya daga cikin irin wadannan kararrakin da ake yadawa a yayin zaben inda ya ce: Masu kirkiro wannan maganar suna kokari ne wajen nuna cewa wasu daga cikin al'ummar Iran suna goyon bayan majalisa ‘yar gwamnati ce, wasu kuma suna adawa da majalisa ‘yar gwamnati. Alhali kuwa al'ummar Iran ba majalisa ‘yar gwamnati suke ba, sannan kuma ba wacce ba ‘yar gwamnatin suke so ba.
Ayatullah Khamenei ya jaddada cewar: Al'ummar Iran dai suna son majalisa ce wacce ta kumshi ‘yan majalisa ‘ma'abota addini', masu aiki tukuru, jarumai, ba wadanda aka yaudara ba, masu tsayin daka da gwagwarmaya wajen tinkarar wuce gona da irin ma'abota girman kai, masu kare daukaka da ‘yancin kasa, masu kaunar ci gaban kasar nan na hakika, wadanda suka yi amanna da yunkuri na ilimi da irin kwarewar da matasa suke da ita, masu amanna da kuma dogaro da tattalin arziki na cikin gida, wadanda suka san matsalolin mutane, wadanda suka kuduri aniyar magance matsalolin mutane, haka nan kuma wadanda ba sa tsoron Amurka sannan kuma masu aiki da nauyin da doka ta ba su. Jagoran ya ci gaba da cewa: Irin wannan majalisar ce al'ummar Iran suke so, ba wai majalisa mai goyon bayan wane da wane ba.
Daga nan sai Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da makirce-makircen Amurka bayan yarjejeniyar nukiliya da aka cimma inda ya ce: Bayan fara aiwatar da yarjejeniyar nukiliya, Amurkawa sun kasance sun tsara wani tsari saboda Iran da kuma wani tsarin saboda wannan yankin, wanda kuma suna nan suna ci gaba da aiki wajen cimma hakan. Don kuwa sun san wace kasa ce ta tsaya kyam wajen tinkarar bakaken manufofinsu a yankin nan.
Ayatullah Khamenei ya bayyana cewa amfani da hanyar tsoma baki da tasiri cikin harkokin cikin gidan Iran a matsayin daya daga cikin makirce-makircensu a kan Iran inda ya ce: Daga lokacin da aka gabatar da batun tsoma baki da son tasirin makiya budu da kari kan yin taka tsantsan da hakan, nan take wasu a cikin gida suka nuna damuwarsu da cewa mai ya sa a koda yaushe ake magana kan tasirin ‘yan waje. To amma babu wani dalili na nuna irin wannan damuwa ta su.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Batun kokarin yin tasiri dai wani lamari ne na hakika, to amma a wani lokaci shi kansa mutumin da aka yi tasiri a kansa ba ya fahimtar hakan da kuma tafarkin da aka dora shi a kai.
Haka nan yayin da yake ishara da maganar marigayi Imam Khumaini na cewa a wasu lokuta a kan sami wasu mutane masu fadi a ji suna maimaita maganganun makiya, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: shi wannan mutumin mai fadi a jin ba tare da ya karbi kudi ko kuma yin alkawari ba, to amma ba tare da ya sani ba yana sake nanata maganganun makiya. Wanda a hakikanin gaskiya hakan wani nau'i ne na share fagen kutsawa da yin tasirin makiya a cikin gida.
Ayatullah Khamenei yayi ishara da wasu misalai na irin wadannan kokarin kutsawa da yin tasiri ba tare da su kansu mutanen sun fahimci hakan ba, daga nan sai ya ce: A shekarun da suka gabata, a fili daya daga cikin ‘yan majalisa, a zaman majalisar, ya ke sake nanata maganar makiya da tuhumar gwamnatin Musulunci (ta Iran) da karya.
Haka nan yayin da yake ishara da wani misalin na daban, Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa yayi: A lokacin da tawagar kasarmu a wajen tattaunawar nukiliya suke tattaunawa mai wahalar gaske wanda a hakikanin gaskiya suna tinkarar daya bangaren ne, wanda shugaban kasa na yanzu ma shi ne shugaban tawagar Iran wajen tattaunawar, kwatsam sai ga wasu sun gabatar da wani kuduri a majalisa da ke goyon bayan abin da daya bangaren (da muke tattaunawa da shi din) yake fadi ne. A wancan lokacin shugaban kasarmu na yanzu ya nuna damuwarsa kan wannan kudurin, da bayyana cewar hakan wani lamari ne da zai taimaki makiya.
Don haka sai Jagoran ya kirayi dukkanin al'ummar Iran musamman jami'ai da ‘yan siyasa zuwa ga yin taka tsantsan dangane da wannan kokari na kutsawa da yin tasiri na makiya yana mai cewa: Wajibin wannan taka tsantsan da sanya idon shi ne cewa idan makiya, saboda cimma manufarsu a tsakanin mutane, suka kasance suna jinjinawa kungiya kaza ko kuma wani mutum, to kamata yayi cikin sauri ba tare da bata lokaci ba ya nuna kiyayya da barrantansa ga hakan.
Ayatullah Khamenei yayi ishara da maganar marigayi Imam Khumaini (r.a) da ke cewa "Matukar makiya suka yabe ka, to lalle ka yi shakku cikin halaye da ayyukanka" inda ya ce: Wannan maganar dai wata doka ce ta juyin juya hali. A saboda haka wajibi ne cikin gaggawa a barranta daga jinjinawar makiya, sannan kuma kada a shagala da hakan.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Wajibin gudanar da wannan kasa mai irin wannan girma da kuma ciyar da al'amurran mutane gaba, shi ne yin taka tsantsan, zama a farke da kuma tsayayyiyar azama wajen tinkarar makiya.
Har ila yau kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi jami'ai da ‘yan siyasa zuwa ga nesantar nanata maganganu da matsaya ta siyasa ta makiya musamman amfani da Kalmar ‘masu tsaurin ra'ayi' da ‘masu sassaucin ra'ayi' yana mai cewa: Tun farkon nasarar juyin juya halin Musulunci, makiya suke amfani da wadannan kalmomi. Abin da suke nufi da masu tsaurin ra'ayi shi ne wadanda suke riko da koyarwar juyin juya halin Musulunci da kuma tafarkin marigayi Imam Khumaini. Sannan abin da suke nufi da masu sassaucin ra'ayi su ne mutanen da suka mika kai ga ‘yan kasashen waje.
Ayatullah Khamenei ya ce: Mutanen da a cikin gida ma suke amfani da wadannan kalmomi, wajibi ne su karanci ilmummukan Musulunci. Don kuwa a Musulunci babu irin wannan rarraba. Ma'anar tsaka-tsaki shi ne ingantaccen tafarki, tafarkin gaskiya. A saboda haka kishiyar ‘yan tsaka-tsaki ba shi ne masu tsaurin ra'ayi ba, face dai wadanda suka kauce daga tafarkin gaskiya.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Mai yiyuwa ne a lokacin da ake kan tafarkin gaskiya, a samu wasu suna tafiya da sauri sosai, wasu kuma a sannu-sannu, wanda babu matsala cikin hakan.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: A mahangar siyasar ‘yan kasashen waje, suna kiran Da'esh ma da kungiyar masu tsaurin ra'ayi, alhali kuwa ‘yan Da'esh wasu mutane ne da suka kauce daga tafarkin Musulunci, Alkur'ani da kuma tafarkin gaskiya.
A karshen wannan bangare na jawabin nasa, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Mutanen da a wajen kasar nan suke amfani da Kalmar masu tsaurin ra'ayi, abin da suke nufi shi ne kungiyoyi masu riko da juyin juya halin Musulunci da kuma tafarkin Ubangiji. A saboda haka wajibi ne a cikin gida a yi taka tsantsan wajen nanata wadannan kalmomi don kada a taimaka wa makiya cimma manufarsu.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da abin da Amurkawa suke fadi na cewa a Iran babu wani mai sassauci, Jagoran ya bayyana cewar: Al'ummar Iran dai masu kaunar juyin juya halin Musulunci ne, sannan kuma sun tsaya kyam wajen riko da shi. Koda yake mai yiyuwa ne a wasu lokuta a samu ‘yan kura-kurai da kauce wa hanya. To amma babu wani da yake son su (makiyan) da kuma goya musu baya.
Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da yanayin zaben yana mai cewa: Duk yadda sakamakon wannan zabe na ku ya kasance, shin kun zabi wanda ya dace ne ko kuma wanda bai dace ba, komai dai yana hannunku ne. A saboda haka ku yi kokari wajen ganin an yi zabe mai kyau.
Har ila yau Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi al'ummar da su yi kokari wajen neman yardar Allah yayin zaben, kamar yadda kuma ya kiraye su da su sanya ido da kuma amfani da basira da sanin ya kamata yayin zaben.
A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jinjinawa irin Imani, gaskiya, sadaukarwa da tsayin dakan mutanen garin Najafabad tsawon lokacin juyin juya halin Musulunci.
Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musulunci, sai da Hujjatul Islam wal Muslimin Hasanati, Limamin juma'ar garin Najafabad din ya gabatar da jawabinsa inda yayi ishara da irin kokarin da mutanen garin suka yi a lokacin nasarar juyin juya halin Musulunci, kallafaffen yaki da kuma sadaukar da sama da shahidai 2500, daga nan sai ya ce: a halin yanzu ma mutanen garin Najafabad din suna nan kan alkawarinsu na riko da koyarwar Musulunci, Alkur'ani da kuma tafarkin marigayi Imam Khumaini da Jagoran juyin juya halin Musulunci, sannan kuma har zuwa karshe suna daram a kan wannan alkawari na su.