IQNA

16:47 - February 29, 2016
Lambar Labari: 3480192
Bangaren kasa da kasa, bangaren bincike na cibiyar Azahar ya bayyana cewa an amince da wani kudiri dangane da yadda za a rika buga kur’anai a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sadal Balad cewa, Muhyiddi Afifi shugaban bangaren bincike kan harkokin addini na cibiya Azhar ya bayyana cewa, sun dauki matakan da suka dace wajen buga kwafin kur’ani mai tsarki.

Wannan mataki dai ya zo ne sakamakon buga wasu kwafin kur’ani mai tsarki da aka yi bisa kure, wanda kuma tuni aka bayar da umarnin tattara su baki daya.

Muhyiddin ya ce daga cikin abubuwan da aka yi ta kai ruwa rana kansu har da buga kur’ani da launuka daban-daban, amma shi a cewarsa bai amince da hakan ba, sai dai da yake malamai sun amince babu matsala za a iya yi.

Daga karshe ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an tabbatar da cewa an bi dukaknin kaidojin da aka kafa wajen buga kur’ani, domin kauce ma sake fadawa cikin kurakuran da aka yi aka a yi a baya.

3479228

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: