
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga Press TV cewa, an gudanar da wannan gangami da jerin gwano a biranan da dama da ska hada da Zaria, kaduna, Yola da kuma Kano, inda ake yin kira ga gwamnatin Najeriya da ta saki Sheikh Zakzaky da take tsare da shi tun tsawon watanni kusan uku da suka gabata.
Abdulhamid Bello daya daga cikin waedanda suka jagorancin gamgamin ya bayyana cewa suna nan kan bakansu na neman ganin an saki malamin nasu ba tare da wani bata lokaci ba.
Masu gangamin sun fitar da wani bayani da ke cewa, an kashe mata da yara kanana. Wani da ya je mucuwaren Asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika Zariya ya fadi cewa ya ga gawawwakin ’yan uwa mata tamanin, kafin sojoji su zo su kwashe su. Cikin yara kanana kuwa da ake da tabbacin kashe su da sojoji suka yi har da Batula Buhari Jega, yarinya ’yar shekara daya da rabi kacal.
An kashe daliban Jami’o’i, Kwalejojin kimiyya da fasaha, Kwalejojin ilimi da makarantun sakandaren da har yanzu ba a kai ga kididdige su ba. Amma Dandalin dalibai na Harkar Musulunci ya fadi a gangamin da ya yi a Abuja kwanan nan cewa, suna da kididdigar bacewar dalibai 30 da suke Jami’o’i da manyan makarantun gaba da sakandare.
An kashe ’yan uwa musulmi sama da dubu guda. Tabbaci hakika akwai sunayen mutane 750 da kawo yanzu ake da su, wadanda ba a gan su ba tun bayan ranar Asabar sha biyu ga Disamba, 2015.
Kawo yanzu babu gawa ko daya da gwamnatin Tarayya ta ba iyalai da dangin wadanda sojoji suka kashe. Bilhasali ma Janar Buratai cewa ya yi wai mutum bakwai kawai suka kashe.
An harbi Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky har sau shida. An kuma harbi matarsa, Malama Zeenah Ibrahim sau biyu a jikinta.
An raunata ’yan uwa musulmi maza da mata bila adadin. Wadanda Allah ya yi da sauran kwanansu, kuma yanzu haka ko dai sun gama jinya, ko kuma suna cikin ta.
An azabtar da ’yan uwa musulmi maza da mata da nau’o’in azabtarwa kala-kala. Mafi muni shi ne kware wa ’yan uwa mata hijabi da sojoji suka yi, da ma zargin yin fyade ga wasu ’yan uwa mata da suka kashe daga bisani.
An yi rusau din nan ne tare da barin barayin gari su sace duk wani abu mai amfani a wadannan wurare. Wasu marasa imanin ma har kudade da zobuna da wayoyin mamatan da ke wuraren suka sace.
Wannan fa a takaicen takaitawa ne muka kawo su. A halin yanzu kuma sai ga shi ana zama a Hukumar binciken wannan tua’annati da sojoji suka yi, alhali an danne wa Jagoranmu, Shaikh Ibraheem Zakzaky damar da tsarin mulki da duk wata doka ta shari’a a kasar nan suka ba shi na ya gana da Lauyoyinsa. Lauyoyin nan sun jejje inda ake tsare da Shehin Malamin har sau hudu, amma ana dakile bukatarsu na su gana da shi.
Lsy Framen daya daga cikin masu kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya yace abin yana tattare da matukar hadari.