IQNA

Babban Taron Kur’ani Na Kasa Bangaren Daliban Jami’a A Masar Karon Farko

22:48 - March 04, 2016
Lambar Labari: 3480202
Bangaren kasa da kasa, ana shirin fara gudanar da baban taron kur’ani na kasa baki daya na matasa yan jami’a akasar Masar karon farko a jami’ar Aminya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwafd cewa, taron zai hada da bangaren hardar dukkanin kur’ani, da kaidojin karatu Tajwidi da kuma sauran ilmomin addini, wanda daliuban jami’oi 19 za su halarta.

Bayanin ya ce Asharaf Shikhi ministan mai kula da harkokin imi mai zurfi da kuma Jamaluddin Abu majd shugaban jami’ar Alminya za jagoranci taron.

Haka nan kuma za a mayar da hankali kan wasu lamrra da suka shafi al’adun addinin muslunci, wanda daliban jami’a masu gudanar da nazaria wannan bangaren za su takara rawa.

Jamluddin Abu Majd ya bayyana cewa, ya zama wajibi a samar da wani shirin irin wannan a kasar, domin kwaakwao bukatar a kara himma wajen wayar da kan matasa musamman yan jami’a da ake ganin za su zama shugabannin al’umma nan gaba.

Ya ce yana da kyau a rika kara karfafa gwiwar matasa wajen shiga duk awani abu na bincike da Karin ilimi a dukkanin bangarori, musamman na ilimin kur’ani mai tsarki.

3480404

captcha