
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Mi’at Bahrain cewa, a jiya dubban al’ummar kasar Bahrain ne suka gudanar da gangami a cikin yankunan kasar musamman ayankin Diraz domin yin Allawadai da zaluncin masarautar kasar a kansu da kuma kira majalisar dinkin duniya da ta dauki matakin takawa mahukuntan kasar birki.
A cikin rahoton da majalisar dinkin duniya ta fitar da kanta kana bin da yake faruwa abahrain, ta bayyana cewa mahukuntan kasar suna danne mabiyar mazhabar shi’a wadanda su ne masu rinjaye a kasar.
Daga cikin abubuwan da ake yi musu kuwa har da rusa musu masallatai da wuraren ibada da kuma cin zarafinsu da iyalansu, da hana su bayyana ra’ayinsu, wanda hakan yake tabbatar da cewa babu yacin fadar albarkacin baki a kasar.
Duk da irin wanann sheda da majalisar dinkin duniya ta bayar da kuma wadanda ta bayar a lokutan baya kan wadanda suke garkame a gidajen kaso na masarautar kasar saboda akidarsu ko mahangarsu ta siyasa, wannan bai sanya kasashen duniya sun dauki wani mataki kan wannan lamari ba.
Maimakon hakan kasashen da suke mara baya ga Bahrain kan kisan kiyashin da take yi kan al’ummarta, sun kara rubanya wannan taimako ne da nufin ganin wanan masarautar mai kare manufofinsu ta cio gaba da dawwama.
Rashid Bin Abdullah Al Khalifa ministan harkokin cikin gidan kasar ta Bahrain a wani furuci da ya yi jiya akasar Tunisia ya bayyana mabiya mazhabar shi’a da cewa su yan bidi’a ne, kuma ba za su taba barin yan bida’a su wala a cikin kasashensu ba.