
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo ENewsPF cewa, babbar cibiyar musulmi a kasar Amurka ta fitar da wani bayani da ke cewa, kalaman batunci kan musulmi da dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican Donald Trump ke yi a yakin neman zabe, sun jawo karuwar kyamar musulmi da kuma cin zarafinsu a cikin kasar ta Amurka.
A wata zantawa da ta hada shi da tashr taklabijin ta CNN Donal Trump ya bayyana cewa, a ganinsa addinin musulunci baya kaunarsu.
Nahad Iwad shugaban majalisar zartarwa ta musulmin Amurka ya bayyana cewa, irin wadannan kalamai da Trump yake sn taimaka matuka wajen yada kiyayya da musluncia fadin kasar Amurka.
Ya ce babban abin takaici ne yadda suka kan musulunci da msuulmi ya zama wani babban makami na yakin neman zabe a kasar da ke raya cewa ita tafi kowa dimukradiya a duniya.
Haka nan kuma ya yi kira ga da a kare hakkokin muslmi a duk inda suke a Amurka, domin kuwa a kowane lokaci rayuwarsu da mutncinsu da dukiyoyinsu suna cikin hadari, sakamakon nuna musu kiyayya da ake yi a kasar.
Majalisar musulmin Amurka ta ce Donal Trump ya jefa miliyoyin musulmi a kasar Amurka da suke zaune lafiya acikin hadai a halin yanzu sakamakon kalamansa na batunci a kansu.
A cikin shekara ta 2015 sau 70 ana kai hari kan masallatan musulmi, wanda shi ne mafi muni a cikin shekaru 7.