IQNA

An Gurfanar Da Dan Siyasar Kasar Holland Mai Kiyayya Da Musulunci

23:30 - March 19, 2016
Lambar Labari: 3480245
Bangaren kasa da kasa, Geert Wilders dan kasar Holland mai tsananin kiyayya da addinin muslunci wanda ya shirya fim na tozarta kur’ani ya gurfana a gaban shari’a.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na France24 cewa, ya gurfana a gaban kuliyar kuwa saboda cin zarafin ‘yan kasar Morocco musulmi mazauana kasar Holland.

Wannan kuwa yana da alaka da wasu kalamai da ya yi ne a cikin shekara ta 2014 a kansu, dangane da yadda yake kallonsu, inda ya yi Magana da ke nuna kyama a gare su.

Babban alkalin kotun kasar Holland ya bayar da umarnin bincike wannan file domin hkunta Wilders bisa wannan furuci, inda ya bayyana cewa hakika wannan kalami na Wilders yana da mummunar manufa akan wadanda yake Magana a kansu.

A cikin shekara ta 2010 an gurfanar da Wilders a gaban kuliya saboda cin zarafin muslmi marassa rinjaye a kasar ta Holland.

A lokacin ya nuna wani fim da ya shirya da ya kira fitina inda yake danganta hakan da kur’ani mai tsarki, wanda littafi da mabiya addinin muslunci suke girmamawa, wanda hakan ya sabawa dokokin kasar Holland.

Bayan nan kuma Wilders ya gabatar da wani daftarin kudiri a gaban majalisar dokokin kasar ta Holland, wanda shi ma acikinsa ya ci zarafin mabiya addinin muslunci, tare da wulakanta su.

3484199

captcha