IQNA

23:50 - March 29, 2016
Lambar Labari: 3480273
Bangaren kasa da kasa, Kotun kolin kasar Bangladesh ta yi watsi da bukatar da wasu suka gabatar mata da ke neman a cire muslunci daga matsayin addinin kasar a hukumance.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Shafaghna cewa, bababr kotun Bangladesh ta yi watsi da bukatar da wasu suka gabatar mata da ke neman a cire muslunci daga matsayin addinin kasa.

A zaman da kotun ta gudanar a birnin Daka, ta bayyana bukatar da mabiya wasu addinai marassa rinjaye a kasar suka gabatar, da ke neman a cire musulunci a matsayin addinin kasar a hukumance, tare da mayar da kasar mai bin tsari da babu ruwansa da wani addini.

Mutanen kasar Bangladesh wadanda kimanin 90% musulmi ne, sun nuna rashin amincewarsu da wannan bukata, inda kungiyoyin addini mafi girma akasar suka kirayi gangami da bore matukar dai kotun kolin kasar ta amince da wannan bukata.

Tun bayan da kasar Bangladesh ta balle daga kasar Pakistan a cikin shekara ta 1971, an gina kasar kan tsari da babu ruwansa da addini, amma a cikin shekara ta 1988, shugaban BangladeshHussain Muhammad Irshad ya mayar da muslunci a matsayin addini kasar a hukumance.

3484812

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: